Labaran Jiha

Majalisar Dokokin Kano ta Amince Da Sauya Sunan KUST Zuwa Jami’ar Kimiyya ta Dangote

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muhammad Adamu Abubakar

Majalisar Dokokin ta jihar Kano ta Amince da dokar saunya Sunan Jami’ar Kimiyya da fasaha ta jihar Kano dake garin Wudil (KUST) zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Dangote dake garin Wudil.

Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na yau talata 11 ga Watan disambar 2022.

Hamisu Chidari ya ce amincewar ta biyo bayan karatu na uku na kudirin dokar wacce akawun majalisar Alhaji Garba Bako Gezawa ya yi Kuma aka Amince da kudirin yayin zaman majalisar na sirri.

Da yake tattaunawa da ‘yan jaridu, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari ya ce an amince da sauya sunan ne la’akari da yadda Alhaji Aliko Dangote ya ke bada gudun mowar cigaban Jami’ar.

Ku karanta: KANO: Chidari Ya Mika Ta’aziyar Rasuwar Mahaifin Shugaban Ma’aikata.

Ya ce Dangote ya dauki nauyin gudanar da ayyukan gina-gine da tsare-tsare da ma dukkan sauran ayyukan cigaban Jami’ar.

A yayin zaman na wannan Rana, majalisar ta bayyana Karbar wata takarda daga Babban Mai binciken kudi na jiha game da rahoton asusun jihar na karshen shekarar 2021.

Majalisar ta Mika rahoton ga kwamitin ta na kula da dukiyar al’umma wanda aka basu umarnin Mika rahoton su a Watanni uku.

Leave a Comment