Addini

Madrasatul Ihya’us Sunna Littahafizul Qur’an Ta Yi Sauka Al’qur’ani Da Walima Na Dalibai 13 a Bagwai

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Shua’aibu Sani Bagwai

Sananan Malamin addinin musulunci a yankin Karamar hukumar Bagwai da kewaye Malam Ibrahim S. Wada Gadanya ya bukaci daliban ilimi su mayar da hankali wajen yin amfani da ilimin da suka samu Maimakon yin alfahari da yawan karatu.

Malam Ibrahim Gadanya wanda kuma shine limamin Masallacin Juma’a na JIBWIS da ke garin Gadanya a Karamar Hukumar Bagwai ya bayyana bukatar hakan lokacin da yake yin ta’aliki kan falalar neman ilimi a wajen taron walimar saukar Alkur’ani mai girma na dalibai 13 na MADRASATUL Ihya’us Sunnar Littahafizul Qur’an da ke Bagwai.

Malam Ibrahim S. Wada Gadanya ya bayyana cewa tarin karatu ba shine ilimi ba, ilimi shi ne mutum ya san Allah sannan ya bi umarninsa a dukkan al’amuransa na rayuwa.

Malamin ya kuma bayar da misalai da dama kan falalar neman ilimi daga cikin Alkur’ani mai girma da hadisan Annabi SAW da kuma yadda za a yi aiki da ilimin.

Ku Karanta: Kulawar Iyaye ce Hanyar karfafa Gwiwar Malamai Don Bada Ingantaccen Ilimi — Hafizu Garko

Tun da farko a jawabinsa tsohon Shugaban Makarantar na farko, Malam Bunyaminu Umar Bagwai ya ce tun daga lokacin da aka kafa Makarantar ta Sami nasarori da dama musamman ta fuskar koyarwa da karantar da dalibai a bangaren addini da zamantakewar rayuwa.

Malam Bunyaminu Umar Bagwai ya kara da cewa duk da nasarorin, Makarantar na fuskantar babban kalubalen rashin mazauni na din-din-din wanda a yanzu haka tana da adadin dalibai fiye da 600, a don haka ya bukaci hukumomi da masu hannu da shuni da kuma iyayen dalibai su taimakawa Makarantar don ganin ta mallaki mazauninta na din-din-din.

Ku Karanta: Sarkin Kano Ya Yabawa Kokarin Kungiyar Tsofaffin Daliban Shahuci

Malam Aminu Lawan Da’awa shine wanda ya gabatar da darasun karatu ga daliban da suka yi walimar saukar.

Taron walimar saukar ya sami halartar mutane daban- daban wadanda suka hada da Shugabannin siyasa da na makarantun Islamiyya da iyaye da kuma ‘yan uwa da abokan arziki.

Leave a Comment