Da Dumi-Dumi

Ma’aikata ya kamata Gwamnatin Tarayya ta karawa albashi da kudin Tallafin Mai – Kwamared Ayuba

Daga: KABIR GETSO

Shugaban kungiyar kwadago (NLC) ta Kasa reshen Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Sulaiman yace kamata yayi Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da kudaden tallafin Mai domin karawa ma’aikata albashi.

Ya bayyana Hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar dake cikin garin Kaduna inda yace tuni kasashen duniya shirin su yayi nisa wajen tabbatar da biyan mafi karancin albashi ga ma’aikata a kaso mai tsoka ta yadda ma’aikatan zasu samu walwala wajen gudanar da ayyukansu.

kwamared Ayuba ya kara da cewa, karancin albashi na naira dubu 30 a lokacin da litar mai na kasa da naira 200 ba isar ma’aikata yake ba, ballantana a yanzu da litar man ta koma 500 da doriya, wanda hakan ya kara ta’azzara tsadar kayayyakin amfani na yau da kullum, don haka yanzu kamata yayi Gwamnatin Tarayya ta dawo da mafi karancin albashi zuwa naira dubu dari biyu N200,000.

Ayuba ya yabawa sabuwar gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Gwamna Uba Sani bisa yadda ya samar da sababbin tsare-tsare da zasu taimaki ma’aikatan jihar, ya kuma bayyana shirin su na tafiya kafada da kafada da tsarin gwamnatin da zai taimaki al’ummar Jihar Kaduna baki daya.

Ya kuma shawarci ma’aikatan da suyi aiki tukuru don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, domin amana ce suka dauka ga gwamnatin domin aiki ga al’umma yadda ya kamata.

Leave a Comment