Labaran Jiha

Kwalejin Koyar Da Aikin Jinya, Unguwar Zoma Dake Birnin Kudu Ta Samu Sahalewar Wasu Manyan Kwasa-kwasai

Written by Admin

Bayanin hakan na kunshe ne a zantawar manema labarai da Shugaban Kwalejin Alh. Garba Adamu Buji, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kwalejin Alh. Hamza Abubakar.

Hamza Abubakar yace, kwalejin tayi shura wajen yaye kwararrun Ma’aikatan jinya da unguwar zoma da sauran sassan bangarori na lafiya wanda hakan ke basu damar samun sahalewar sabbin kwasa-kwasai daga Hukumar kula da kwalejin kasarnan.

Ya kara da cewar, daga cikin sabbin kwasa-kwasan da aka sahale akwai Babbar Difuloma akan aikin jinya da unguwar Zoma (Post Basic Midwifery)
wato duk wadanda suka kammala karatun aikin jinya a baya zasu iya dawowa domin karin samun horo akan aikin unguwar Zoma na tsawon watanni 8.

Hamza Abubakar ya yabawa Gwamnatin jihar Jigawa karkashin Shugabancin Gwamna Malam Umar A. Namadi bisa irin kyakkyawan tsari da manufofi da yake samarwa Musamman a bangaren makarantun Lafiya na jihar.

Musamman la’akari da yadda Kwalejin ta samu tsangaya har uku daga ciki akwai Cibiyar kwalejin dake Birnin Kudu sai tsangayar Kwalejin koyan aikin jiya dake Hadejia sannan sai tsangayar Kwalejin koyan aikin unguwar Zoma dake Babura, kuma kowacce tsangayar an tanadar mata Kyakkyawan tsari domin cigaban duk Masu hudda da kwalejin.

Kwalejin ta koyar da aikin jinya da unguwar Zoma dake Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa na kara kira ga dukkanin masu sha’awar shiga kwalejin daga ko’ina dake fadin kasar nan da cewa kofa a bude take, su Shiga manahajar Kwalejin domin su damar shiga don samun ingantaccen ilimin lafiya a fannonin aikin jinya da unguwar Zoma.

Leave a Comment