Yanzu-Yanzu

Kwalejin Kimiyyar lafiya da fasaha dake Ningi na taka Muhimmiyar rawa a kasarnan – Alh Garba Husaini

 

By: KABIR GETSO.

Shugaban Kwalejin kimiyyar lafiya da fasaha ta Ningi dake jihar Bauchi (College of Health and Technology) Alhaji Garba Husaini (DAN BABASCO). Ya bayyana Kwalejin a matsayin wata garkuwa ga al’ummar kasar nan wajen samar da Nagartattun Dalibai masu sanin makamar Ilimin lafiya.

Magatakardan Kwalejin Malam Aliyu Hassan wanda shine ya wakilci Shugaban kwalejin a lokacin tattaunawa da manema labarai a Kwalejin, yace idan akayi la’akari da tarihin kwalejin, tun daga matakin farkon kafa ta har zuwa wannan lokaci kullum samun daukaka take, a fannoni da dama tare da samun sahalewar sabbin kwasa kwasai wanda hakan ke kara samun tururruwar Dalibai daga sassa daban daban dake fadin kasar nan.

Malam Aliyu Hassan ya kara da cewar, Saboda kwazon kwalejin a shekara ta 2020 Daliban sashin gwaje gwaje wato medical Laboratory kaso 98 cikin dari ne suka lashe jarabawa, kazalika Daliban National Diploma wanda suma kaso 98 cikin dari suka lashe jarabawa.

Sai bangaren Post Graduate Diploma wanda kaso 100 cikin dari ne suka lashe jarabawa, haka abin yake a bangarori da dama na kwalejin. Yace dukkanin wadannnan nasarori suna samuwa ne bisa jajircewar Shugaban makarantar da sauran malamai wanda kullum ake dauki ba dadi don ganin an fita kunyar al’umma.

Magatakardar ya yabawa Gwamnatin Jihar Bauchi Karkashin Shugabancin Gwamna Bala Muhammad Kauran Bauchi, bisa irin kokarinsa na samawa kwalejin kayan aiki da sabbin gine gine domin dorewar bunkasar kwalejin don anfanuwar al’ummar jihar dama kasarnan baki daya.

Shugaban Kwalejin ya ja hankalin Daliban da su kasance jakadu nagari wajen aiki tukuru da maida hankali don dorewar cigaban Kwazon kwalejin a idon al’umma, tare da kaucewa duk wata mummunar dabi’a da zata zub da darajar kwalejin a idon duniya.

Kazalika ya yi kira da sauran masu rike da madafun iko da sauran masu hannu da shuni da su cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen kokarin tallafa kwalejin a fannoni da dama.

Leave a Comment