Ilimi

Kwalejin Horar Da Jinya Da Ungozoma Ta Kano Ta Yaye Dalibai Kusan 200

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Kamal Yakubu Ali

Shugabar rukunin makarantun horar da kiwon lafiya da Ungozoma ta jihar Kano dake Danbatta da Gwarzo da kuma kwaryar birnin Kano ta bukaci daliban da aka yaye dasu Tabbatar sun bada gudun-mowar da ta da ce wajen bunkasa harkokin lafiya a fadin jihar Kano da ma kasa baki daya da nufin samun alumma ta Gari.

Shugabar Makarantar Dakta Mairo Sa’id Muhammad ta bukaci hakan ne a bikin yaye dalibai karo na biyu na dalibai 197 wadanda suka fito daga makarantun gwarzo, Dambatta da kuma jihar Kano.

Ta ce makarantun suna bada gagarumar gudanmawa wajen samar da kwararrun maaikatun jiya da  ungozoma a fadin jihar nan domin tallafawa gwamnati wajen shawo kan matsalolin da mata suke fuskanta a lokutan goyan ciki da kuma haihuwa, domin samun alumma Mai koshin lafiya.

A nata  bangaren Shugabar reshen makarantar dake kwaryar birnin Kano Hajiya Munubiya Abdullahi jibril ta bukaci daliban da suka kammala karatun dasu zamanto wakilai na Gari a duk inda suka kasance, domin aikinsu ginshikine na samar da alumma Mai cike da koshin lafiya.

Ku Karanta: Madrasatul Ihya’us Sunna Littahafizul Qur’an Ta Yi Sauka Al’qur’ani Da Walima Na Dalibai 13 a Bagwai

Dalibai 196 ne dai aka yaye Wanda suka Hadar da 48 daga makarantar dake cikin Birnin Kano, da kuma Dambatta da take da dalibai 70, Sai kuma Gwarzo mai dalibai 78.

Shugabar ta bayyana irin matsalolin da makarantun ke fuskanta wadanda suka hadar da Rashin hasken wutar lantarki da matsalar mota inda ta bukaci gwamnati Data kawo musu dauki.

Da yake jawabi Farfesa Umar sani Fagge Wanda malam Nazir Adamu ya wakilta ya bukaci daliban da suka kammala karatunn da suyi amfani dashi wajen tallafawa yan uwansu mata musamman wadanda suke zaune a karkara domin magance matsalolin da suke fuskanta a lokutan goyan ciki da kuma haihuwa.

Ku Karanta: Kulawar Iyaye ce Hanyar karfafa Gwiwar Malamai Don Bada Ingantaccen Ilimi — Hafizu Garko

A yayin taron an karrama wasu daga cikin malamai, dalibai da ma aikatan makarantar wadanda sukeyi fice  wajan bada gagarumar gudanmawa a bangarori da dama ciki harda Aisha Salisu Gwarzo da Malama Rabi da kuma Malam Ahmad Ibrahim.

Taron ya samu halarta alumma da dama wadanda suka hadarda shugaban kungiyar kwadago ta jihar Kano Kwamared Kabir Ado Munjibir sai kuma wamban Bichi injiniya sani Abdulkadir da  Zubairu idris Danbatta da sauran alumma da dama.

Leave a Comment