Da Dumi-Dumi

Kungiyar ‘Yan Jaridu Mata Ta Shirya Gangamin Wayar Da Kai Ga ‘Yan Makarantu Ayayin Bikin Ranar Yara

Written by Pyramid FM Kano

Daga: JAMILU SULEIMAN ALIYU

Kungiyar mata ‘yan jaridu reshen jihar Kano hadin gwuiwa da asusun tallafawa kananan yara sun gudanar da gangamin wayar da kai ga yara ‘yan makaranta akan mahimmancin da karatunsu yake dashi da kuma mahimmancin rigakafin cutar cancer musamman ta mahaifa da ake fatan fara bayar da riga kafin ga yaran da suka kama daga shekaru tara domin sune shekarun mafarin kamuwa da cutar.

Dukkan taron wani bangarene na bikin ranar yara ta duniya. Inda Dr. Radiyya Bashir Kasim wadda ta kasance likitace a asibitin Murtala. Tayi jawabi mai tsawo akan hadarin cancer da kuma yadda riga kafin zaiyi tasiri ga ‘ya’ya mata duba da, cutar su take kamawa. Inda ta kara bayyana cewa, ana basu riga kafin ne tun kafin susan ma’amalar aure domin a nan ake dauka kuma tana nunawane tun a shekaru ashirin da biyar zuwa arba’in da tara, a don haka suke jan hankalin yaran su guji ma’amala da yara maza tun a matakinsu na karatu, su maida hankalin su akan karatunsu.

A daya bangaren, Hajiya Hafsat Sani Usman, ta bayyana mahimmancin wannan gangamin wayar dakan da cewa, zai taimaka ne domin yaran zasu kai sakon da suka samu inda ya dace duba da ba duka yaran jihar aka hadu dasu ba tayi kira ga ‘yan jaridu da su taimaka su isar da sakon wasu yara inda Rediyon Pyramid FM ta zanta dasu sun bayyana jin dadinsu da wannan taron tare da shan alwashin aikata abin daya dace dangane da karatunsu mahalatta taron sun hadar da likitoci da shugabannin makarantu da masana akan fannin lafiya da malaman makaranta.

Leave a Comment