Da Dumi-Dumi

Kungiyar Tsoffin Daliban Sakandaren Kawaji (KOBA 1988) Ta Gudanar Da Taronta Na Shekara

Written by Admin

By: MUHAMMAD ADAMU ABUBAKAR 

Kungiyar tsofaffin daliban makaratar sakandire ta Kawaji ta Maza wato Government Secondary School Kawaji Boys (KOBA) ajin na 1988 ta gudanar da Taron su na shekara shekara.

Shugaban kungiyar Alhaji Adamu Musa Tarauni ya bukaci daukacin ‘yan Kungiyar da su cigaba da bayar da kyakyawan hadin Kai ga tafiyar ta su domin samun nasarar kungiyar.

Kungiyar tsofaffin daliban ta saba gudanar da Taron ne duk karshen shekara domin sada zumunci dama duba abubuwan da makaratar take da bukata domin bayar da tallafin da za su iya.

Da ya ke bayyana makasudun taron nasu mataimakin shugaban kungiyar Auwal Alhaji Muhammad ya ce kasancewar ‘ya ‘yan kungiyar wasu Allah Ya Yi musu rasuwa, bisa haka ya zama wajibi su zabi wasu domin cike gurbin su.

Shi ma mai bayar da shawara a fannin shari’a ga kungiyar Umar Faruk Sale ya bayyana cewa abin farin ciki shi ne duk alkawaruka da suka dauka a shekarar data gabatar sun samu nasarar cika su.

Taron ya gudana ne a harabar makaratar sakandiren dake Unguwar Dakata a Karamar hukumar Nasarawa, cikin birnin Kano wanda ya samu halartar ‘yan ‘yan kungiyar da dama.

Leave a Comment