Da Dumi-Dumi

Kungiyar Matukan Motocin tanki ruwa Sunyi Sabbin Shuwagabanni a Kano

By: KABIR GETSO

Kungiyar Matukan Motocin Tankin Ruwa wato (Kano Water Tanker Drivers Association) Tayi zaben sabbin shuwagabanni a nan Jihar Kano, kwamared Abdussalmu Salisu Rimin Gado shine ya lashe zaben da kuri’u mafi rinjaye.

Da yake jawabi bayan kammala zaben ya sha alwashin kawo tsare-tsare da zasu cigaba da tafiyar da kungiyar cikin kyakkyawan yanayi da zai taimaki mambobin kungiyar dama al’ummar Jihar Kano baki daya.

Kwamared Abdussalmu yayi kira da sauran wadanda basu samu nasara ba a wannan zabe da su zo a hada hannu wajen ciyar da kungiyar gaba.

Kazalika, ya roki Gwamnatin Kano da ta basu cikakken goyon baya don bunkasar sana’ar tasu, yace akwai abubuwa da dama da za’a tallafawa matuka tankunan ruwa wadanda suka hada da shigowar gwamnati cikin harkar samar da ruwa da samar da guraren fakin ga direbobin da kuma sama masu sabbin motoci bashi suna biya a hankali da kuma hada su da kamfanoni domin aiki da su kai tsaye.

kwamared Rimin Gado ya yabawa Gwamnaatin Jihar Kano bisa yadda ta fara Ayyuka da ke taba al’ummar Jihar baki daya wanda ya nuna irin cika alkwari da Gwamnatin tayi tun Lokacin yakin neman zabe.

Shima a nasa Jawabin Mataimakin Kakakin Majalisar jihar Kano Alh. Muhammadu Bello Butu-Butu, ya yabawa kungiyar bisa yadda take bada gudummuwa wajen samawa matasa ayyukan yi da rage radadin wahalar ruwa da wasu tankunan birnin kano ke fama da shi, tare da tabbatar masu da cewa Gwamnatin jihar kano zatayi duk mai yiwuwa wajen ganin ta share masu hawaye a bukatun da suka bayyana.

Kazalika ya yi kira ga saura sabbin shuwagabannin da su jajirce wajen aiki tukuru don ciyar da kungiyar gaba.

Leave a Comment