Da Dumi-Dumi

Kungiyar matuka motocin Haya ta Kasa Reshen Malam Kato ta bayyana godiyarta ga Gwamnatin Jihar Kano kan Dawowa da masu sana’o’i wurarensu a cikin Tashar

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen Malam Kato, ta bayyana godiyarta ga Gwamnati da hukumar kula da tsara birane da karkara na jihar Kano, bisa yunkurinsu na dawowa da al’ummar da suka rasa guraren sana’o’insu dake cikin Tashar ta Malam Kato.

Shugaban kula da binciken kudade na Kungiyar Alh. Samaila Giredi ne ya tabbatar da haka a lokacin da kungiyar ta shirya taron manema labarai, dangane da gine-ginen da wasu mutane suke yi ba bisa ka’ida ba.

Yace, sakamakon gine-ginen da aka yi ya sanya Dubun jama’a sun bar guraren da suke cin abinci a cikin Tashar wadanda akasari magidanta ne, inda yace, bayyana direbobi akwai masu harkar kasuwanci.

Samaila yace, bisa hakan ne kungiyar ta nuna farin cikinta saboda tsayar da ginin da wasu masu hannu da shuni suke yi, wanda ya farune gaf da Gwamnatin da ta gabata za ta tafi.

Shugaban yace, sai dai kuma Allah ya tausawa bayin sa da suke neman abincinsu a Tashar, bisa tausayi da hangen nesa da Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf take da shi na taimakawa Wanda aka zalunta.

Ya kuma bayyana cewa, Kungiyar Direbobin ba za ta gajiya ba wajen bin dokokin da Gwamnati da masu ruwa da tsaki akan wannan lamari domin ciyar da jihar Kano gaba ba musamman ta fannin sana’ar  ‘yan kungiyar.

Yace, za su yi amfani da wannan dama wajen baiwa Gwamnati tabbaci domin hada hannu na samar da kudaden shiga wanda da sune Gwamnati take ayyukan ci gaba da za su taimaki al’umma.

Haka zalika, ya bukaci ‘yan kungiyar Tashar ta Malam Kato da su kara himmatuwa wajen baiwa Gwamnatin Jihar Kano hadin kan da suka kamata da ma ita kanta Kungiyar Direbobin, wanda yin hakan zai haifar da bunkasa harkokin sufuri da samar da ayyukan yi ga matasan da basu da aiki a fadin jihar nan.

Yace, yanzu lokaci ya yi da ya kamata kungiyar ta ba da gagarumar gudunmawa ga Gwamnatin da hukumomin kula da harkokin sufuri na jihar domin ta yi gogayya da sauran kasashen ketare da suke habbaka bangarori daban-daban musamman bangaren da suka shafi tuki.

 

Leave a Comment