Manyan Labarai

Kungiyar Masu Siyar Da Littattafai Ta Jihar Kano, Ta Koka Akan Rashin Samun Wasu Littattafai A Kasuwanni

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar masu sana’ar siyar da littattafai ta jihar Kano, ta koka da yadda wasu makarantu masu zaman kansu suke hada da wasu kananan kamfanoni marasa rijista da Gwamnati wajen samar da littattafai da babu su a kasuwanci tare da tursasa iyayen yara su siyesu komai tsadarsu a fadin jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar a kasuwar Sabon Gari Kwamared Umar Musa Gama ne yayi koken a lokacin da kungiyar ta gudanar da taron manema labarai a nan jihar Kano.

Yace, kungiyar masu siyar da littafai ta jihar Kano, ba za ta zuba ido ba, irin wannan katobara na faruwa acikin jihar Kano ba, saboda hakan zai kara gurgunta harkokin ilimi a jihar nan.

Yace, duk da kiraye-kirayen da iyayen yara suke yi dangane da wannan lamari, amma hakan bata sauya zani ba, domin iyayen yara suna fuskantar kalubale duk da matsin rayuwar da al’ummar suke ciki.

Wata mata da ‘ya’yanta suke zuwa makarantu masu zaman kansu, Hajiya Ummi Yakasai, ta bayyana damuwarta akan wahalar da take fuskanta, musamman wajen neman littattafan da aka rubutowa ‘ya’yanta ta fannin tsada da wahalar samunsu a kasuwanni.

Tace, saboda sun yi wahalar samu dole iyayen yara suke komawa makarantun domin siyansu a cikin tsada domin ganin sun sauke nauyin daya rataya akansu, saboda babu yadda za su yi.

Sai dai mun tuntubi shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu, Injiniya Adamu Aliyu, dangane da wannan lamari, yace, bashi da damar yin magana akan zarge-zargen da ake yi masu na boye littattafai domin gallazawa iyayen yara.

Idon za’a iya tunawa,maitaimakawa Gwamna Kano, a fannin makarantu masu zaman kansu, Baba Umar, yana ta zagaye zuwa makarantu masu zaman kansu domin ganewa idonsa akan wadan nan zarge zarge da ake yiwa makarantun.

Haka zalika, Baba Umar, ya sha alwashin kawo karshen irin wadannan matsalolin da suke faruwa a fannin harkokin ilimi a jihar Kano, wanda yana daga cikin abubuwan suke durkusar da ilimi da kuma, hana ‘ya’yan talakawa karatu.

 

Leave a Comment