Kasuwanci

Kungiyar Masu Siminti Ta Gamsu Da Bude Iyakokin Kasar Nan

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar ‘yan kasuwa masu sana’ar siyar da siminti ta Karamar Hukumar Ungogo ta nuna tsantsar farin cikinta bisa yadda gwamnati tarayya ta Amince a shigo da wasu kayayyakin masarufi zuwa cikin kasar nan.

Daya daga cikin ‘yan kwamatin masu sana’ar Alh. Bashir B.T.D ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Gadar Rimin Kebe a nan Kano.

Alh. Bashir ya bayyana cewa, mutane da dama suna ta tunanin cewa, ba’a bude iyakokin Kasar nan ba, wanda kuma, tuni Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni har ma da yin alkawarin baiwa yankasuwa Dala daga Bankin Kasa.

Bashir BTD yace, sakamakon bude iyakokin da aka yi,Alumma za su samu saukin al’amura wajen gudanar da hada hadarsu ta yau da kullum da kasuwanci da farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Yace, akwai bukatar gwamnatoci su taimakawa al’umma wajen wayar musu da kansu yadda ya kamata domin su fahimci gaskiyar abubuwan da aka amince a shigo da su daga cikin kasashen ketare.

Ya kuma, bukaci kungiyoyin ‘yan kasuwa da daidaikun Al’umma, da su kasance masu tausayawa jama’a a koda yaushe da zarar an samu saukin kayayyaki.

Daga karshe, ya shawarci al’ummar Najeriya da su kasance masu gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da samun saukin rayuwa duba da halin da al’umma suka samu kawunansu dangane da matsin rayuwar da ake ciki.

Leave a Comment