Kasuwanci

Kungiyar Masu Kananan Masana’antu Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Na Bude Boda

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Hukumar Gudanarwar Kungiyar masu kananan masana,antu ta jihar kano,ta bayyana gamsuwarta da umarni da Gwamnatin tarayya ta bayar na shigo da wasu daga cikin kayayyakin masarufi zuwa cikin kasar nan.

Shugaban kungiyar Ibrahim Bashir na Sambo ne ya bayyana haka a yayin ganawarsa da manema labarai dangane da bude iyakokin kasar nan da baiwa yankasuwa Dala Wanda ya gudana a ofishinsa dake rukunin kamfanonin Sharada.

Ibrahim Bashir yace,indai wannan tsari da Gwamnatin ta amince da su,zai samu kulawa to lallai za’a samu gagarumar nasara wajen shigo da kayayyaki daga kasashen ketare, Wanda kuma,kasar za ta samu saukin abubuwa,musamman yadda kayayyakin masarufi suka yi tashin gwauran zabi a fadin kasar nan.

Wakilin mu Ibrahim Sani Gama ya bamu rahoton cewa Shugaban yace, Masu Kananan Masana’anutu a jihar kano, suna Neman hadin kan Gwamnatin tarayya da ta jiha wajen ganin an tallafawa masu kananan Masana’antu dake nan jihar kano ,kasancewar suna fama da rashin cikakken jari da kayayyakin aiki irin na kasashen ketare.

Ibrahim Bashir yace, lokaci yayi da Gwamnati za ta dubi kananan masana’antun jihar kano kasancewar suna mutukar ragewa Gwamnatoci a matakai daban_daban nauye nauye ta bangaren marasa Ayyukan yi da suka yi yawa a lunguna da sakuna na Kananan Hukumomin jihar kano.

Shugaban yace, Rashin samun Sana’a a gurin Matashi da rashin Zuwa Makaranta suna bashi damar yin tunanin Abubuwan da zai aikata domin Neman mafita a cikin Rayuwarsa.

Alh Ibrahim Bashir Sambo,ya yabawa Gwamnatin jihar kano da ta ke kokarin ta Tura Daliban jihar kano zuwa kasashen ketare domin Neman Ilimi,Domin ilimi shine yake kara seta rayuwar ‘Yanadam a kodayaushe.

Haka Zalika,Ya bukaci Gwamnatin jihar kano da ta tarayya da su hada hannu da Rukunin Kamfanoni dake Sharada,Saboda Gudunmawar da suke bayarwa a kodayaushe a ciki da wajen jihohin.

Yace, Kungiyar masu kananan Masana’ntu ta jihar kano,ta jaddada kudirinta na hada hannu da Gwamnatoci a matakai daban daban domin Neman hanyoyin da za ta saukakawa Alumma da samarwa ‘Ya’yanta mafita da su rika sarrafa kayayyakin masarufinsu da samarwa matasa ayyukan yi da samarwa Gwamnatin Kudaden haraji yadda ya kamata.

Daga karshe Shugaban Kungiyar, Ibrahim Bashir Sambo, ya bukaci yankungiyar,da su kasance masu baiwa kungiya da Hukumomin Gwamnati da suke da hannu a Fannin cikakken hadin kan da ya kamata domin samun damar ciyar da kungiyar gaba.

Leave a Comment