Da Dumi-Dumi

Kungiyar Masu Hada-hadar Magunguna Dake Malam Kato Ta Goyi Bayan Hukumomin Dakile Gurbatattun Magunguna A Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar masu hada hadar magunguna ta kasa reshen jihar Kano dake kasuwar Malam Kato a nan birnin Kano, ta jaddada bayar da goyan bayanta ga Hukumomin dake da alhakin kawar da gurbatattun magunguna a jihar Kano.

Shugaban Kungiyar Mohammed Musbahu Yahaya ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da wani rahoton da wasu suka fitar a kafafen sadarwa akan ‘ya’yan Kungiyar.

Shugaban yace, kungiyar masu hada hadar magani ba za ta zuba ido wasu daidaikun mutane da ba su da alaka da sana’ar siyar da magani su rika shafawa ‘ya’yanta kashin kaji ba.

Yace, sakamakon gabaren da kungiyar kasuwar magani ta jihar Kano, ta dauka na ganin an kawo sauyi a bangaren sana’ar, sai wasu mutane da suke bukatar sai sun durkusar da kananan ‘Yan kasuwar da basu da karfin jari suka bijiro da Sai Alumma sun koma kasuwar Dangwauro wadda ta fi karfin da yawa daga cikin ‘Yan kasuwar.

Mohammed Musbahu, ya bayyana cewa, wadanda suke da bukatar sai al’umma sun tashi sun koma kasuwar dake Dangwauro, sun hada kai ne da wasu masu ruwa da tsaki akan kasuwar ta Dangwauro, inda suka zuba kudadensu a matsayin hannun jari domin Durkusar da Kananan masu karamin jari da Leburorin dake fafutukar neman yadda za su ciyar da iyalansu da ‘Yan uwansu.
A don haka, shugaban yace, hshugabancin kungiyar ba zai gajiya ba wajen fitar da batagarin mutane daga cikin ‘Yan kasuwar magani domin samar da kyakyawan yanayi da taimakawa yunkurin gwamnati mai ci na kakkabe baragurbi dake safarar muggan kwayoyi da kasuwancin magunguna da wa’adinsu ya kare domin al’ummar jihar Kano da ma kasa baki daya su samu magunguna da kare lafiyar al’umma.

Shugaban kungiyar kasuwar maganin ya kara da cewa, kungiyar da ta zo a cikin kashi dari na masu shigowa da gurbatattun magunguna, ta magance kashi tamanin da biyar ta yin hadin gwuiwa da Jjmi’an tsaro da suka hadar da Hukumar Hana sha da Fataucin miyagun kwayoyi da jami’an ‘Yan Sanda da sauran Hukumomin dake da hurumi akan dakile gurbatattun magunguna ta hanyar hsamar da kwamati na musamman da yake yawo lungu da sako na kasuwar domin gano masu sana’ar ba bisa yadda doka ta tanada ba.

Daga karshe shugaban yayi kira da Gwamnati, da sauran hukumomin dake da alhaki akan wannan lamari da su kawowa ‘Yan kasuwar magani daukin gaggawa musamman, kananan Yankasuwar, bisa zalinci da wasu masu hannu shuni suke son yiwa kananan ‘Yan kasuwar da wadanda suke leburanci domin ciyar da iyalansu da kuma, sharrin da suke kokarin kullawa al’ummar, hwanda kuma, ba dai dai bane.

 

Leave a Comment