Manyan Labarai

Kungiyar Manyan Motocin Haya Zata Cika Alkawarinta Akan Gwamnatin Tarayya

Written by Admin

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar manyan motocin haya ta jihar Kano ta jaddada kudirinta na baiwa gwamnatin tarayya cikakken hadin kan da ya kamata wajen samar da kudaden shiga domin tabbatar ci gaba a fannin harkokin sufuri a kasa baki daya.

Shugaban kungiyar masu haya na manyan motoci na jihar Kano reshen Tafawa Balewa acikin kwaryar birnin Kano Alh. Yakubu Ibrahim Adamu Gizina wanda ya wakilta mataimakinsa Alhaji Halliru Ibrahim Gizina ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da yunkurin gwamnati na rage wasu kudade a bangaren sufuri wanda ya gudana a babban ofishin nasu.

Halliru Ibrahim yace, rage kudade a bangaren sufuri abune da zai taimaka gaya wajen samar da ayyuka ga matasa a fadin jihar da ma kasa baki daya, inda yace, idan aka yi duba na tsanaki za’a ga mutane da yawa ne ke dogaro da bangaren na sufuri.

Za’a samu sauki da yawa, musamman ta bangaren siyan man fetur da gas da sauran abubuwa da masu motoci suke bukata, wanda za su yi amfani da kudaden da aka rage musu wajen aiwatar da wasu bukatun.

Shugaban ya bayyana cewa, su kansu Direbobin ya kamata su kasance masu kulawa da motar da suke aiki da ita da kayayyakin da aka doro musu, musamman a wannan lokacin na hunturu da aka tsinci Kai.

Yace, lokacin karshen shekara Kuma lokaci ne daya kamata a rinka kiraye-kiraye garesu saboda yawan haddura da ake samu kan titina sakamakon yawan tafiye-tafiye da ake yi domin zuwa hutun karshen shekara.

Halliru Ibrahim Gizina ya shawarci matuka motocin haya da kaucewa gudun wuce sa’a domin yin tsere da abokan mu’amulla wajen nuna kwarewa.

Yace, sau da yawa wasu daga cikin direbobin manyan motoci ana dora musu kayayyakin da sun fi kudin motar. Amma sai ka ga suna tukin ganganci da rayuka da dukiyoyin al’umma wajen nuna bajinta.

Halliru Ibrahim ya bayyana cewa, masu A.A. Gizina suna yawan shirya taro domin wayar da kan al’umma, musamman direbobi wajen sanin makamar aiki da sanin abubuwan da suka kamata domin samun ilimi da horo akan abubuwa da suka danganci harkokin tuki.

Shugaban kungiyar ya yi kira ga gwamnati ta jihar Kano da ta tarayya, da su bijiro da wasu hanyoyi da su taimaka wajen hada hannu da mamallaka motocin haya wajen ba su ayyukan da za su bunkasa harkokin sufuri a kasar nan da bunkasar tattalin arziki na kasa baki daya.

Yace, ya kamata gwamnati ta fahimta cewa, harkokin sufuri na daya daga cikin managartan abubuwa da suke samar da kudade da dama wadanda za su ciyar da kasa baki daya.

Ya jaddada cewa, kasashen duniya da dama suna samun makudan kudaden da ke baiwa gwamnati damar aiwatar da ayyukan raya kasa da bunkasar tattalin arziki, musamman wajen samar kayayyakin more rayuwa da su kara ciyar da kasa gaba kamar sauran gakwarorinsu.

Yace, gwamnati na da rawar takawa ainun wajen wadatar motoci a kungiyoyin domin baiwa direbobi da suke da kwarewa kuma, suke neman aikin da za su rika yi, wadanda su kansu sai sun samu wasu da za su rika aikin tare.

Haka zalika, Halliru Ibrahim, ya koka akan rashin kyawawan hanyoyin da ake da su a fadin kasar nan, wanda yace, rashin kyawun hanya na ba da cikakkiyar gudunmawa wajen afkuwar haddura da wasu jihohin ke da su a dukkannin fadin Najeriya.

Daga karshe, yayi fatan Allah ya zaunar da Kasar nan lafiya tare da yin kira ga al’umma wajen yiwa shugabanni da kasa addu’o’in samun zaman lafiya mai dorewa domin neman samun sauki daga wajen Allah mahalicci, duba da wahalar da al’ummar Najeriya suke ciki.

Ya kuma, bukaci hadin kan ‘ya’yan Kungiyar da su ci gaba da fadakar da direbobi musamman sababbi cikinsu duba da yawan korafe-korafen da ake kalubalantarsu akan tukin ganganci da gudun wuce za’a lokacin da suka hau hanya domin yin tafiya.

Leave a Comment