Manyan Labarai

Kungiyar Manoma Alkama Tayi Sababbin Shuwagabanni – Rinji

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar manoman Alkama ta kasa Reshen jihar kano, ta jaddada aniyarta na bunkasa harkokin noman Alkama a fadin kasar nan.

Shugaban kungiyar na kasa reshen jihar Kanno, Alh. Hashimu Abdullahi Rinji ne ya bayyana haka a lokacin da kungiyar take kaddamar da shugabancinta na kananan hukumomi wanda ya gudana a nan Kano.

Hashimu Abdullahi yace, kungiyar ta kammala dukkannin shirye-shiryenta na fara gudanar da noman Alkama a dukkannin fadin kasar nan, shi yasa kungiyar manoman Alkaman za ta fara gangamin wayar da kan manoma Alkaman ta yadda za su kara samun ilimi a fannin harkokin nomansu.

Yace, akwai tsare -tsare masu mahimmanci da za su taimakawa manoman na Alkama a kasa baki daya, wadanda suka hadar da zamanantar da harkokin noman na Alkama da tallafawa kananan manoma domin samun damar cin gajiyar wannan sabon tsari.

Hashimu Abdullahi Rinji, ya yi kira ga kafatanin manoman na Alkama dake fadin kasar nan, da su zo domin yin rijista da wannan kungiya, kasancewar yanzu lokaci ya sauya, shi yasa shugabancin kungiyar manoman Alkama ya zo da Kyawawan shirye-shiryen da za su taimaka tare da inganta harkokin masu noman Alkama a fadin kasar nan.

Hashimu Rinji ya kara da cewa, kungiyar ba za ta gajiya ba wajen hada kai da gwamnatoci a matakai daban-daban wajen nemowa ‘ya’yanta abubuwan da za su habaka musu nomansu ta hayoyin da suka kamata wajen ganin al’umma sun ci gajiyar shirin tun daga matakin kananan hukumomi da jiha da ma kasa baki daya.

A jawabinsa sakataren kungiyar, Ali zakari kura, ya bayyana cewa, kungiyar ta kasa baki daya za ta kaddamar da shirin fara gudanar da noman Alkama na jihohi daga ranar Talata mai zuwa a garin Maiduguri dake jihar Borno, wanda daga nan ne za’a shigo sauran jihohin dake fadin kasar nan.

Ali Zakari Kura ya bayyana cewa, wannan kungiya itace halastacciyar kungiyar manoman Alkama da take da rijista da gwamnati tun daga matakin kananan hukumomi da jihohi da tarayyar kasar nan.

Sakataren kungiyar ya shawarci dukkannin manoman Alkama na lungu da sako da su zo a hada hannu guri guda domin samun damar cin gajiyar shirin da nasara a bangaren noman Alkama.

Yace, wannan dama ce da manoman Alkama suka samu wajen inganta harkokin bomansu, inda yace, yin rijista da kungiyar za basu damar bunkasar nomansu yadda ya kamata da kuma, samun ilimi da tallafe-tallafe daga hukumomin gwamnati daban daban.

Daga karshe yayi kira ga ‘ya’yan wannan kungiya da su ci gaba da baiwa gwamnati da shugabancin kungiyar manoman Alkama cikakken hadin kan da suka kamata domin ciyar da noman Alkama gaba, tare da mayar da asar Najeriya ta yi gogayya da sauran Kasashen duniya da suka yi fice a bangaren noman Alkama.

Leave a Comment