Da Dumi-Dumi

Kungiyar Fagge Progressive Alliance Ta karrama Farfesa Bashir Muhammad Fagge

Daga: KABIT GETSO

Shugaban kungiyar Alh Haruna Usman Fagge yace sun shirya wannan taron ne don karrama Farfesa Bashir Muhammad Fagge wanda shine mai taimakawa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Jibrin akan sha’anin Manufofi da bin diddigi duba da irin jajurcewarsa wajen ciyar da al’umma gaba da samawa matasa Ayyukan yi.

Alh Haruna ya kara da cewa wajibi ne a rinka fito da alkairan irin su Farfesa Bashir Muhammad Fagge domin hakan ya zama izina ga sauran masu dama irin tasa da su himmatu wajen tallafawa al’umma da matasa baki daya,

Farfesa Bashir Muhammad Fagge mutun ne da kafin barinsa aiki ya samawa matasa ayyuka a fannoni da da dama kuma a matakai da dama na tarayya da kuma Jiha,don haka wannan kungiya na kira ga sauran al’umma da suyi koyi da Farfesa Bashir Muhammad Fagge.

Daya daga cikin manyan bakin da suka halarci taron Shugaban Ma’aikatan Ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Farfesa Muhammad Bin Abdullah ya yabawa wannan kungiya inda yace lallai tayi abinda ya dace wajen karrama Farfesa domin mutum ne da ya kamata ya zama abin koyi ga sauran al’umma duba da hazakarsa da na son cigaban al’umma.

Shima a nasa jawabin Farfesa Bashir Muhammad Fagge ya nuna godiya ga Allah bisa wannan rana da al’umma suka taru, tare da yabawa wannan kungiya bisa yadda take kokarin cigaban yankin nata, ya kuma sha alwashin cigaba bijiro tsare tsare na cigaban matasa da kuma sauran al’umma baki daya.

Farfesa Fagge ya ja hankulan matasa akan kaucewa duk wasu muyagun dabi’u da zasu kai mutum su baro shi inda ya kara da cewar matasa sune ginshikin al’umma don haka kamata yayi a tashi tsaye don magance duk matsalolin da zasu addabi al’umma.

Taron ya samu halartar manya mutane na ciki da wajen jihar Kano.

Leave a Comment