Labaran Jiha

Kungiyar CISLAC Ta Gudanar Da Taro Kan Yawaitar Ciyo Bashi Da Gwamnatin Keyi

Written by Admin

Daga: Abdulmajid Isah Tukuntawa

An gudanar da taron manema labarai lalubo mafita dangane da yadda za’a takaita yawan ciwo bashi da gwamnatoci keyi da kuma bada shawarar yadda za’a biya bashin da aka karbo na baya.

Taron Wanda ya kasan ce karkashin hadin gwuiwar Tax Justice and Governance Platform Kano with support of Civil Society Legislative Advocacy Center (CISLAC).

Ayayin taron, an gabatar da matsala dangane da halin tattalin arziki ya tsinci kansa a ciki, wnda kuma yawaitar ciyo bashi na daya dagaci kin dalilan durkushewar tattalin arzikin da ake fama dashi wanda aka gabatar da mahawara don magance al’amarin ciwo bashin da akeyi batare da gano illar da hakan yake yi ba.

A nasa jawabin, Babban Darakta Muh’d Mustapha ya yi kira na musaman ga shuwagabanni da masu iko da su dubi halin da al’umma suka tsinci kansu na matsin rayuwa, inda yayi roko da akalli rayuwarsu a taimakesu don suma su sami ingantacciyar rayuwa.

Taron ya samu hallartar kungiyoyin mata da Kuma sauran kungiyoyin gwagwar maya a fadin Kasa.

Leave a Comment