Labaran Jiha

Kungiyar Bibiyar Haraji Da KIRS Sun Gudanar Da Taron Bita Ga Masu Ruwa Da Tsaki Kan ‘Yancin Biyan Haraji a Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Rabiu Sanusi

Kungiyar Bibiyar Haraji da akafi sani da Tax Justice and Government Platform hadin gwuiwar hukumar tattara haraji ta jihar Kano sun shirya taron bita na kwana daya ga masu ruwa da tsaki kan batun nauyin da ya rataya da Yancin masu biyan haraji a jihar Kano.

A jawabin sa shugaban kungiyar bibiyar karbar haraji da aikin da shi na jihar Kano kuma shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya da dorewar dimukuradiyya da akafi sani da (DAG) Dr. Mustapha Muhammad Yahaya yayin taron yace lallai yakamata al’umma su fahimci cewa sai da kudi gwamnati take da damar gudanar da ayuka ga Jama’ar ta.

Sakataren na kungiyar tuntuba ta Arewa na jihar Kano watau (ACF) ya kara da cewa idan har al’umma za su biya haraji kamar yadda yakamata to lallai Gwamnatin zata tabbatar tayi aikin da ya kamata a matakin ta.

Amma Dr. Mustapha ya bayyana cewa lallai al’umma na zargin gwamnatin kan rashin gudanar ma da jama’a aiki, sai dai wannan matsalolin suna faruwa ne ta hanyar da yawa mutane basa biyan harajin ta hanyar da ta dace.

“Anan nake kira ga wadanda suka samu damar zuwa wannan bita dasu koma anguwanni su dan wayar ma da al’ummar ku kai kan wannan batu dan samun sanayya akan haka.”

A cikin takardar da Sadiq Muhammad Mustapha ya gabatar yayin taron bitar yace lallai kudaden da ake biya na haraji sune gwamnati take you ayukan da suke ga Jama’ar kasa.

Malam Sadiq yace ayukan da gwamnati za su yi sun hadar da gina asibitoci, Makarantu, Hanyoyi, Ruwan sha,Batun Tsaro,habaka noma da kiwo, da sauran su.

A jawaban wakilan hukumar karbar haraji ta jihar Kano watau Darakta Abba da shugaban kwamitin karbar haraji na kananan Hukumomi 44 na jihar Kano Sarki Kurawa sun bayyana ma wadanda suka halarci taron banbanci tsakanin Tax da Levy’s.

Haka Kuma a taron an ba hukumar tattara haraji na jihar Kano shawara kan tayi kokarin shirya zama da ziyarar masu manyan kantina na manyan kasuwannin jihar Kano dan basu damar biyan haraji da zai habbaka tattalin arzikin a jihar Kano.

A wannan zama dai ya nuna mahalarta taron sun tattauna abubuwa masu amfani da zasu bunkasa hanyoyin tattara kudin shiga a jihar Kano.

Taron dai ya gudana a dakin taro na margayi Malam Aminu Kano dake Gwammaja, an kuma tattauna batutuwa masu ma’ana, haka kuma wannan taro hadin gwuiwar kungiyoyin Tax Justice Government Platform da KIRS DAG wanda Christian Aid suke taimakawa da wajen daukar nauyin ayukan.

Leave a Comment