Ilimi

Kulawar Iyaye ce Hanyar karfafa Gwiwar Malamai Don Bada Ingantaccen Ilimi — Hafizu Garko

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Shugaban makarantar Sayyidi Abubakar Siddiq Lil-Ilmi Wattarbiyya da ke Unguwar Gini a karamar hukumar Birnin Kano Malam Hafizu Muktar Garko ya bayyana kulawar iyaye a matsayin hanyar karfafa gwiwar Malamai Don bawa Yara Ingantaccen Ilimi Addini da na Zamani.

Hafizu Garko ya bayyana haka ne yayin bikin saukar karatun Alkur’ani Mai tsarki na daliban makarantar su 61 karo na Uku.

Ya ce malaman makarantu na samun kwarin guiwa a sha’anin bai wa yara ilimi idan har akwai samun kulawar iyaye ta hanyar ziyartar makarantu a Kai a Kai domin sanin halin da yaran su ke ciki da uwa-uba samar musu da kayan karatu da kuma biyan kudaden makaranta akan lokaci.

Ku karanta: Kulawa da Marayu Hanya ce Ta Samun al’umma Ta Gari — Bilkisu Yola

Muktar Garko ya kara da cewa makarantar da aka samar a shekarar 2013 tana gudanar da karatu ne da Asuba wajen bai wa yaran da suke Unguwar da sauran makwabta ilimi kusan kyauta idan ban da dan abin da bai taka Kara ya karya ba na kudin laraba.

Bisa haka ne ya bukaci samun daukin sauran al’umma domin samarwa makarantar matsuguni na din-din-din musamman ganin yadda makarantar ke kara habaka a kullum da yawan dalibai.

A jawabansu daban daban madakin Kano hakimin karamar hukumar Birni Alhaji Yusuf Nabahani Cigari da Dokajin Kano hakimin karamar hukumar Garko Alhaji Aliyu Muhammad Wudil sun bukaci al’umma musamman iyaye da su Kara kula a sha’anin tarbiyyar yaransu da ka ilmin su na Addini da na zamani domin samun al’umma ta gari.

Ku Karanta: Za Mu Yi Amfani Da Duk Abin Da Ke Hannun Mu Domin Cigaban Kwalejin CAS — Ali Saadu Birnin-kudu

Shi kuwa malami Mai jawabi a yayin taron kuma limamin masallacin Juma’a na Ja’en Malam Ibrahim Sagagi ya hori daliban da suka sauke Alkur’anin da su kara zage Danse wajen cigaba da neman ilmin addinin musulunci.

A yayin taron an kaddamar da kalandar makarantar tare da bai malaman makarantar kyautar naira dubu 50 daga sarkin fadar Kano hakimin karamar hukumar Tarauni Malam Ado Kurawa da kuma makamanciyar wannan kyauta daga Alhaji Auwal Bello da wasu al’umma domin Kara karfafa musu guiwa.

Leave a Comment