Ilimi

Kulawa da Marayu Hanya ce Ta Samun al’umma Ta Gari — Bilkisu Yola

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Shugabar kungiyar tallafawa marayu da marasa karfi wato “Hope for Orphan and Less – privileged Initiative (HOLPI)” a turance Hajiya Bilkisu Sani Yola ta bayyana kulawa da rayuwar marayu da marassa karfi a matsayin hanyar samun al’umma ta gari.

Bilkisu Yola ta bayyana haka ne ya yin taron kaddamar da Asusun gina makaranta domin bai wa yara marayu da marasa karfi ilimi kyauta da kungiyar ta samar a nan Kano.

Ta ce manufar samar da makarantar shi ne kula da ilimin yara marayu da marasa karfi tun daga tushe har zuwa manyan makarantu kyauta domin su ma idan sun girma su san suma ‘ya’ya ne kamar kowa.

Shugabar kungiyar ta Kara da cewa kaddamar da Asusun ya biyo bayan samun Fili da kungiyar ta yi a unguwar Yola cikin karamar hukumar Birni, da kuma makarantar za ta fara bayar da ilimi kyauta ga marayun da suka fito daga unguwanni 9 da ke makobtaka da unguwar ta Yola.

Ku Karanta: Zamu Goyi Bayan Duk Jam’iyar Da Zata Karbo Hakkin Yan Kungiyar Mu da Aka kashe — Mustapha Ali

Sani Yola ta kuma bayyana irin ayyukan kungiyar na kula da rayuwar marayu da marasa karfi da suka hadar da ciyar da su abinci a duk watan Azumin Ramadan da Kuma ba su kayan sallah gami da raba musu Naman sallah a duk lokacin sallar Layya.

Ta Kara da cewa kungiyar HOLPI ta samu nasarar ciyar da gidaje sama da 500 a wasu daga kananan hukumomin jihar Kano lokacin annobar COVID-19 da kuma gudanar da Aikin Ido kyauta hadin guiwa da kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar kano tare da daukar nauyin karatun wata daliba marainiya da ke karatu a makarantar ilmin aikin jiyya ta jiha.

Ta kuma bayyana cewa kungiyar tun bayan kafata tana samun kudaden shiga ne ta hannun ‘ya’yan kungiyar da kuma tallafi da ga wadansu kungiyoyin tallafawa al’uma da suka hadar da ta Mai dakin shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari.

A jawabinsa na maraba daya daga cikin iyayen kungiyar Alhaji Rabi’u Muhammad Dan Shareef ya bayyana an kafa kungiyar ne domin tallafawa rayuwar marayu da ke cikin al’umma ta hanyar basu ilimin addinin musulunci da na zamani da kuma koya musu hanyar dogaro da Kai domin su amfani Kan su da Kuma al’uma.

Ku Karanta: SAS Ta Bada Gagarumar Gudun Mowa a Rayuwar Mu — Abdullahi Maikano

A sakonnin da suka aike da shi mataimakin gwamnan jihar kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ta hannun kwamishinan raya karkara Alhaji Abdulhalim Dan-maliki da gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ta hannun kwamishinan muhallin jihar Alhaji Hamza Sulaiman Faskari sun yaba bisa samarwa da kungiya musamman domin kula da rayuwar marayu da marasa karfi.

A yayin taron wasu manyan Malaman addinin musulunci da suka hadar da Sheikh Abdulwahab Abdallah da wakilin limamin masallacin Juma’a na Alfurqan Dakta Bashir Aliyu Umar sun gabatar da jawabi kan muhimmacin kula da maraya a addinin musulunci.

Shi kuwa mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Katsina Injiniya Shehu Sulaiman ya bayyana yadda majalisar dokokin jihar ta sahalewa gwamnatin jihar kashe naira miliyan dubu 2 domin tallafawa marayu da ke kananan hukumomin da ke da matsalar tsaro a jihar.

A yayin kaddamar da Asusun gina makarantar, babban Mai kaddamar wa Alhaji Dahiru Barau Mangal ya bayar da gudunmwa mafi tsoka ta naira miliyan 10 sai gwamnatin jihar Katsina Aminu Bello Masari da ya bayar da naira miliyan 3 yayin da mataimakin gwamnan jihar kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya bayar da gudunmwar naira dubu 500 da sauran al’umma da suka bayar da tasu gudunmwar.

Leave a Comment