Addini

Kudirin Masarautar Gaya Kan Sha’anin Addini

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Masarautar Gaya ta jaddada kudirinta na ci gaba da tallafawa Sha’anin Addinin musulunci da sauran ayyuka a yankunan masarauta domin ciyar da yankuna gaba.

Maimartaba Sarkin Gaya Alh. Aliyu Ibrahim Gaya, wanda mai taimaka masa a harkokin sadarwar zamani kwamared Ubaliyo Gaya ya wakilta ne ya bayyana haka a lokacin bude masallacin juma’a dake karamar hukumar Gaya.

Kwamared Ubaliyo yace, masallacin tsohon masallaci ne wanda Maimartaba Sarkin Gaya ya dauki nauyi aka mayar da shi sabo wanda shine aka bude shi a yau tare da yin sallar juma’ar wannan ranar.

Maimartaban yace, masarautarsa ba za ta gajiya ba wajen gudanar da irin wadan nan ayyuka domin ciyar da harkokin musulunci gaba.

A jawabinsa shugaban kungiyar malamai ta jihar Kano Mal. Ibrahim Khalil, yayi kira ga al’ummar yankunan da su kasance masu kulawa da masallacin, inda yace, Masallaci dakin Allah ne dake bukatar kulawa koda yaushe.

Mal. Khalil yace, laifi ne babba a cikin addinin musulunci mutum yaga datti a masallaci ya ki daukewa.

Haka zalika, al’umma da dama ne suka halarci taron bude masallacin na juma’a , wadanda suka hadar da Maigirma Wazirin Sokoto wanda shine ya gudanar da huduba a lokacin sallar juma’ar da aka bude masallacin da ita a karamar hukumar Gaya da hukumomin gwamnati da manya shugabanni masu rike da Masarautun Gargajiya na gida da na wajen da ‘yan kasuwa da dai sauran al’umma.

Leave a Comment