Yanzu-Yanzu

Kudirin Gwamnatin Tarayya Kan Noman Alkama – Rinji

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar masu noman Alkama ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana gamsuwarta da tsarin da Gwamnatin tarayya ta bijiro da shi domin fara kaddamar da noman Alkama na kadada 70,000 a watan Nuwamba mai zuwa a fadin kasar nan.

Shugaban kungiyar masu noman Alkama na kasa reshen jihar Kano, Alh. Hashimu Abdullahi Rinji ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a nan Kano.

Hashimu Abdullahi yace, kungiyar a shirye take wajen yin aiki kafada da kafada da Gwamnatoci a matakai daban daban na wajen wayar da kan al’umma muhimmanci noman Alkama a lungu da sako na birni da karkara.

Kungiyar masu noman Alkaman ta kasa, tana da rijista da Gwamnatin tarayya da ta jiha haka zalika da duk kananan hukumomin dake fadin kasar nan.

Shugaban yace, kasar Najeriya tana da fadi, amma, wannan kungiya ita ce wadda gwamnatin ta amince da ita a matsayin kungiyar da take da kwafin komai a hannunta, kuma kungiya ce da take da duk abubuwan da ake bukata na shedar cikakkiyar kungiya.

Hashimu Abdullahi Rinji, ya kara kira ga al’ummar Kasar nan da suke da sha’awar shiga wannan kungiya, da su zo domin kofa a bude take da zarar suna bukatar hakan.

Daga karshe ya bukaci ‘ya’yan kungiyar masu noman Alkama da su kasance masu hadin kan da ya kamata wajen ciyar da kungiyar gaba yadda ya kamata, inda yace, “kungiyar ta himmatu wajen yin duk mai yiwuwa domin kare muradan kungiyar da ‘ya’yanta a koda yaushe.”

Sannan yace, “kungiyar masu noman Alkaman, Kungiya ce da ta ke son zaman lafiya da kare martabar harkokin noma musamman noman Alkama a ko ina cikin gida Najeriya da sauran kasashen ketare.

Leave a Comment