Yanzu-Yanzu

Ku Yi amfani da kuri’un ku domin zabar shugabanni na gari – Sarkin Kano

By: Mukhtar Yahaya Shehu

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya bukaci al’uma su yi amfani da damar da suke da ita na zabar shigabanni nagari wadanda zasu jagoranci al’uma.

Sarkin yayi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi na musamman ga manema labarai a fadarsa.

Cikin sanar wa mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na masarautar Kano Alhaji Abubakar Balarabe Kofar Na’isa mai martana sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya hori al’uma da su zauna lafiya a lokutan gudanar da zabukan na gwamnoni da’yan majalisun dokokin jihohi da za a gudanar a ranar asabar mai zuwa 18 ga wannan wata na Maris.

Sarkin ya ce sai da Zaman lafiya ne ake iya aiwatar da komai a don haka ne ya hori matasa su kaucewa furta munanan kalamai da amfani muggan makamai tare da shan kayan maye da dukkan wani abu daka iya jirkitar da hankalinsu domin kaucewa abubuwan da ba su kamata ba.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake jaddada bukatar Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni su cigaba da wayar da kan al’umarsu muhimmacin Zaman lafiya.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su cigaba da sanya ido akan dukkan wanda ya aikata wani laifi tare da hukuntashi.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi addu’ar samun zabin shugabanni nagari a dukkan matakan zabubbukan da za a gudanar a fadin kasar nan.

Leave a Comment