Muhalli

Ku Tsaftace Unguwannin Ku Don Yakar Cututtuka, Gwamnatin Kano Ga Al’umma

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SANI MAGAJI GARKO

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokutan tsaftar Muhalli na gobe Asabar don tsaftace muhallin su tare da yashe Magudanan ruwa din yakar kananan Cututtuka da suke damun alumma.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Alhaji Nasiru Sule Garo ne ya bayyana hakan bayan kammala tsaftar Muhalli ta kasuwanni da ma’aikatu da hukumomin gwamnati wacce ake gudanarwa a duk juma’ar karshen wata a Kano.

A wannan watan, Ma’aikatar Muhalli ta ziyarci Ma’aikatar lafiya da Hukumar kula da asibitocin jihar Kano da kuma Ma’aikatar kasuwancin ciniki da masana’antu ta jihar Kano inda Kwamishinan Muhallin ya basu wadansu gyare-gyaren da kwararru a harkokin kula da tsaftar Muhalli na Ma’aikatar suka gano.

“Akwai wasu ‘yan gyare-gyare da muka basu, yawanci inda ake da ‘yan matsalolin bandakuna ne saboda karancin ruwa, ofishin manyan Ma’aikata mun same su cikin tsafta sai dai akwai karancin ruwa, amma na kananan akwai ‘yan gyararrakin da muka basu, kuma mun bukaci manyan M’aaikatan su tabbatar kananan suna kula da bandakunan su da ma na mutanen da suke ziyartar su,” inji Nasiru Garo.

Kwamishinan ya ja hankalin al’umma da su kansance masu bin dokar tsaftar Muhalli da za’a gudanar a gobe Asabar tare da tabbatar sun zauna a gidajen su gami da tsafta ce su.

Nasiru Garo ya kuma yi fatan al’ummar jihar Kano za su rika yashe Magudanan ruwansu akai-akai don tabbatar da tsafta.

Leave a Comment