Lafiya

Ku Tabbatar Da Gwajin Jini Kafin Daura Aure, Hakimin Ajingi Ga Limamai

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Zaharaddeen Saleh.

Hakimin Ajingi a masarautar Gaya dake nan jihar Kano Arewa maso yammacin Nigeria Alhaji Wada Muhammad Aliyu ya Umarci Limamai dake yankin karamar hukumar Gezawa da Minjibir da su daina daura Aure har sai sun tabbatar ma’auratan sunyi gwajin cutar amosani jini wato sikila.

Hakimin na Ajingi wanda kuma shine madakin Gaya ya bada wannan umarnin ne a wajen taron karawa juna sani daya shiryawa Dagatai da Limamai da masu unguwani na kananan hukumomin Gezawa da Minjibir.

Wada Muhammad Aliyu wanda Malam Abdulkadir Abdullahi Zanku ya wakilta, ya ce saboda mahimmacin da gwajin cutar amosanin jinin yasa hakimin Ajingi ya yi taro wayar dakai ga Dagatai da masu unguwanni harma da limamai.

Dakta Bello muhammad na babban asibitin garin Minjibir da Dakta Hamisu Musa Tahir sune suka gabatar da makala akan illar kin yin gwajin da kuma irin wahalar da iyaye zasu sha idan suka haifi yaro mai dauke da cutar Amosanin Jini.

Ku karanta: Amosanin-Jini: Za Mu Tallafawa Masu Cutar Ta Kowacce Hanya — Sarkin Kano

Dakta Bello ya kara da cewa duk wanda yake da jini “AA” baya fuskantar barazar cutar ko kadan, yayin da wadda kuma yake da “As” to yana da Burbushinta wadda kuma yake “SS” yana da cutar don haka mai “As” da Mai “As” da Mai “SS” ba zasu iya yin aure ba.

Shima a nasa jawabin, hakimin minjibir Malam ismail Abdullahi A. Fulani ya sha alwashin wayar dakan alumma yakin karamar hukumar minjibir baki daya.

Leave a Comment