Addini Labaran Jiha Lafiya

Ku Tabbatar da Gwajin Jini Kafin Aure Don Kare Lafiyar ku, ‘Ya’yan Ku — Adamu Gizina

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar wayar da Kai da tallafawa masu larurar cutar amosanin jini ta jihar Kano, bukaci al’umma su tabbatar da Gwamnatin jini ga mata da matasan da ke son yi Aure domin kare yaduwar cutar Amosanin jini da kuma kula da Lafiyar su da ta ‘ya’yan su.

Ta kuma ce za ta ci gaba da gudanar da wayar da kan al’umma da tallafawa masu larurar cutar amosanin jini a Kano da ma Nigeria don yin gwaji kafin aure.

Shugaban kungiyar Maharazu Ibrahim Adamu Gizina ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ci gaba da zagayen da kungiyar take yi a garin Sarauniya dake karamar hukumar Dawakin tofa a nan Kano.

Maharazu Ibrahim ya ce, kungiyar ba za ta gajiya ba wajen wayar da kan matasa maza da mata mahimmancin yin gwajin jini kafin Aure, duba da Matsalar da ake samu yanzu na yaduwar cututtuka daban daban a cikin alumma, musamman cutar amosanin jini da take sanadiyyar mutuwar kananan yara da manya da aka haifa da ita da kuma, irin wahalhalun da iyaye mata suke tsintar kansu a ciki.

Shugaban ya ce sakamakon Illar da cutar amosanin jini take da ita, shi yasa kungiyar ta himmatu don ganin ta tallafawa masu larurar cutar da kuma wayar da kan iyaye mata da maza da su kansu matasa, su rika yin gwajin cututtuka kafin Aure a tsakanin masoya.

Ku karanta: Zamu Sauya Tsarin Koyar da Sana’o’i da NUC ta zo da shi Don Samarwa Matasa Aiki — Farfesa Kurawa

Muharazu Ibrahim ya kuma, bukaci mahukunta da masu ruwa da tsaki a fannoni da dama da kungiyoyi masu zaman kansu da masarautun gargajiya kan su taimaka wajen wayar da kan matasa don yin gwaji kafin aure a cikin birane da kankara, sakamakon Matsalar ake samu ga rayuwar masu larurar.

Ya kuma shawarci masu larurar, kan su rika bin dokokin likitoci a koda yaushe, inda ya ce, ya kamata kuma a rika daina nuna musu kyama kasancewar suna dauke da cutar Sai dai a rika basu shawarwarin da za su kula da kansu da abincin daya kamata su ci da sauran abubuwan da suke amfani da su.

A jawabinsa tun da farko, Dagacin garin Sarauniya, Bashir Magaji, (Magajin Sarauniya) Ya sha alwashin cewa za su Samar da kwamiti na musamman domin ci gaba da wayar da kan matasa maza da mata da iyaye mahimmancin yin gwajin cututtuka kafin aure domin kaucewa kamuwa da cututtuka wadanda Ba, a cika samun magungunansu cikin sauki ba.

Ya kuma umarci masu ungunwanni da dagatai da limamai a garin Sarauniya da sauran garuruwan yankunan da su tabbata duk wadanda suka tashi yin Aure sun yi gwajin cututtuka kafin ma soyayya ta yi nisa har akai da yin kokarin aure duba da yadda Maaurata
Suke shan wahala da zarar an samu cututtuka makamantan irin
wadannan.

Haka zalika, magajin Sarauniyar, ya yi kira ga kungiyar da sauran masu
Hannu da shuni da kuma, Gwamnati kan su kawo musu dauki domin kara Samarwa garin Sarauniya
Asibiti da cibiyoyin bayar da magunguna kasancewar Sun yi musu karanci a garin.

Daga nan ya godewa Shugabancin kungiyar, bisa jajircewar da gudunmawar da yake bayarwa a dukkannin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano.

Leave a Comment