Addini Ilimi

Ku Sanar Da ‘Ya’yan Ku Matsayin Annabi S.A.W, Sahabbai Don Tsira, Sakon Habib Dan-almajiri ga Iyaye

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Kamal Yakubu Ali

Sannen Malamin addinin Musulunci a nan Kano Sheikh Barista Habibu Muhammad Dan-almajiri ya bukaci Iyaye da su rika Sanar da ‘Ya’yan su Matsayin Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da sahabban sa domin samun tsira a rayuwar duniya da ma lahira.

Barista Dan-almajiri ya bayyana hakan a taron mauludin fiyayyen halitta Annabi sallallah Alaihi wasallam wanda ya gudana a Unguwar marmara dake cikin birnin Kano da Kewaye.

Ya ce taron mauludi wata makaranta ce ta Al’qur’ani da kuma sanar da tarinin Annabi sallallah Alaihi wasallam da sahabbansa, da irin gagarumar gudanmawar da suka bayar wajen tabbatuwar addinin musulunci, ta hanyar  zaburar da musulmi domin kwaikwayon rayuwar Annabi da ta sahabbai  domin samun rayuwa ta gari.

Ku karanta: KANO: Chidari Ya Mika Ta’aziyar Rasuwar Mahaifin Shugaban Ma’aikata.

Ya kara da cewa bada labarai na gaskiya a game Annabi sallallah Alaihi wasallam da sahabbansa shine abunda alumma suke bukata domin kaucewa  labarai marasa inganci da wasu mutane suke jinginawa game da sahabbai da sauran bayin Allah na gari.

Barista Dan-almajiri ya bayyana cewa riko da koyarwar addini musulunci da chusa kaunar Annabi data sahabbansa shine mafita wajen samun ingantacciyar rayuwa da kuma kwanciyar hankali a tsakanin alumma a duniya da kuma lahira.

A karshe ya yabawa wadanda suka shirya Taron mauludin, inda ya bayyana cewa dukkannin wanda yayi wata hidima domin Annabi sallallah Alaihi wasallam babu shakka Annabi zai mayar masa acikin karamcinsa.

Leave a Comment