Tattalin Arziki

Ku Kyauta Rayuwar Al’umma Da Kudaden Shigar Ku, Aminu Ado Ga Gwamnatoci

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Matakan Gwamnatoci su rika yin amfani da kudaden shigar da suke samu ta hanyoyin da zasu cigaba ga kyautata rayuwar al’ummar da suke wakilta.

Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin taron kasa na shekara shekara da kungiyar Masana Tattalin arziki ta kasa wato “Nigerian Economic Society” ta shirya a dakin taro na jami’ar Maryam Abacha dake nan Kano.

Sarkin yayi kira ga al’umma su dunga biyan Kudaden da ya kamata su biya ga Gwamnatoci domin da haka ne za’a samun damar gudanar da ayyukan cigaban al’umma.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran masarautar Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya sanyawa hanu ta ambato sarkin na Kano na bukatar ‘ya’yan Kungiyar su sami dangantaka da masu ruwa da tsaki akan sanin Tattalin arziki domin fadada ilimi da dabarun farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Ya ce jihar Kano jiha ce ta cibiyar kasuwanci bawai a arewacin kasar nan ba harma da kasashen duniya baki daya, a don haka akwai rawar da zata taka domin cigaban Nigeria.

Ku Karanta: Za Mu Cigaba Da Bada Gagarumar Gudun Mowa a Bangaren Lafiya — Aminu Ado

Ya ce tuntubar “Yan Kasuwa zai taimaka a samu wani bangare na ilimi wanda zai taimakawa bincike don samun nasarar farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Bayero ya ce irin wannan tattaunawar tana da matukar muhimmanci a wajen al’umma kuma ta haka ne za’a cigaba da wayar da kan mutane hanyoyin da zasu runka biyan haraji.

Ya kuma yabawa shugabannin kingiyar busa kokarin da sukai wajan hada taron na kasa a nan Kano.

Da take nata jawabi, Shugabar kungiyar Farfesa Ummu Ahmad Jalingo ta ce sun shirya taron ne domin tattauna hanyoyin da za’a bi wajen farfado da tattalin arzikin Nigeria.

Ta ce hakan ne ma yasa suka yiwa taron na bana taken yadda za’a tabbatar da da’a wajen sarrafa kudade da hanyoyin da manufofin Gwamnati wajen farfado da arziki.

Masana tattalin arziki daga sassan jami’o’in kasar nan sun halarci taron na bana da Kungiyar ta gudanar.

Leave a Comment