Labaran Jiha

Ku Guji Shiga Bangar Siyasa, Sakon Dan-jummai ga Matasan Kwasangwami

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugabancin kungiyar ci gaban al’ummar garin kwasamgwami dake karamar hukumar Gezawa Alhaji Aminu Dan-jummai ya bukaci matasan yankunan da su kaucewa shiga bangar siyasa, musamman a wannan lokacin da babban zaben shekarar 2023 ke tafe.

Aminu Dan-jummai ya bukaci hakan dangane da yadda harkokin zabuka suke karatowa.

Ya ce kasancewar lokacin zabuka yana karatowa, akwai bukatar kungiyar ta ja hankalin matasan yankunan domin kar su bari wasu yan siyasa su yi amfani da su domin cimma muradunsu a siyasance da kuma, sanya su a cikin yanayi na damuwa da zai haifar musu da matsaloli a rayuwar su.

Ku Karanta: 2023: Za Tabbatar An Zabi Shugabanni na Gari — Gidauniyar Ibrahim Khalil

Ya ce a duk lokacin da yan siyasa suka samu damar darewa kan mulki ba za su tuna da su ba, daga su sai ‘ya’yan su sai yanuwan matansu da sauran wadanda suke bukatar su zo kusa da su, inda ya ce ba’a hana matasan yin zabe ba, amma ya kamata su yi karatun ta nutsu wajen sanin wawannhugaba yakamata su zaba domin inganta rayuwarsu a nan gaba.

Aminu ya ce an dade ana ruwa kasa na shanyewa akan alamuran da suka shafi harkokin matasa da kungiyoyin matasa, kasancewar matasa sune kashin bayan kowacce alumma, dole ne a ci gaba da kiraye kiraye akansu wajen kiyayewa shiga al’amuran da za su sauya rayuwarsu da suka hadar da shaye_shaye da amfani da makamai wajen biyawa wasu bukatunsu, inda ya kara da cewa, jamian tsaro da hukumomi da kungiyoyi suna ta kiraye kiraye a garesu na su kaucewa shiga bangar siyasa, ta kafafen yada labarai.

Haka zalika, ya yi kira ga iyaye da su iya kokarinsu domin sauke nauyin daya rataya a wuyansu kasancewar, Allah subahanahu wata’ala sai ya tambaye su ranar gobe alkiyama, inda ya ce iyaye suna da rawar takawa wajen fadakar da yayan su ta hanyoyi da dama su kuma fahincesu tare da kaucewa shiga bangar siyasa.

Ku Karanta: Kulawar Iyaye ce Hanyar karfafa Gwiwar Malamai Don Bada Ingantaccen Ilimi — Hafizu Garko

Daga nan ya shawarci mahukunta da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin siyasa da su fito da wasu hanyoyi da za su saka matasa akan gwadabe nagari da zai janye hankalin matasan yankuna daban daban na kasar nan, na hada kai da ake yi da matasa wajen yin magudin zabe a yayin zabe da ma bayan zabe.

Alhaji Aminu kwasamgwami ya bukaci alummar kasar nan da su kasance masu gudanar da addu’oin samun zaman lafiya mai dorewa da samun yalwatar arziki.

Leave a Comment