Yanzu-Yanzu

Koyar da Alku’rani nauyi ne Malamai ke sauke wa iyaye – Alaramma Sadisu.

By: Mukhtar Yahaya Shehu.

Shugaban makarantar Tahfizul Qur’an da ke Unguwar Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso Alaramma Muhammad Sadisu ya bayyana koyar da Alku’rani da malamai ke yi wani nauyi ne suke sauke wa iyaye.

Alaramma Muhammad Sadisu ya bayyana haka yayin bikin saukar karatun Alku’rani mai girma na dalibai 40 karo na biyu.

Ya ce sanar da yara ilimin Alku’rani nauyi ne da Allah Ya dora wa iyaye, amma bisa wasu dalilai da Kuma Uzuri na rayuwa malamai ke dauke wa iyaye ta hanyar tura su makaranta.

Shugaban makarantar ya ce yana daga cikin kikari da makarantar ke yi wajen cigaba da zaburar da dalibanta hanyoyin samun ilmin Alku’rani cikin sauki ta hanyar kwarewar malamai a sha’anin koyarwa.

“Sau da yawa duk lokacin da ka halarci bukukuwan saukar karatun Alku’rani a makarantu daban-daban za ka ga dalibai mata ne suka fi yawa, amma mu a makarantar mu lamarin ba haka ya ke ba.” In ji Malam Sadisu.

Ya Kuma ja hankalin iyaye da su cigaba da tallafawa wadannan makarantu a Koda yaushe domin samun nasarar da ake bukata.

A Jawabin sa daya daga cikin iyayen makarantar Barrister Aminu Wudilawa ya bayyana kadan daga cikin tarihin makarantar cewa an kafa ta a shekarar 2015 da dalibai 15.

Barrister Aminu Wudilawa ya ce yana daga cikin nasarar da makarantar ta samu shi ne cikin dalibai 15 da suka sauke karatun Alku’rani a karo na farko fiye da rabinsu a yanzu haka sun Haddace Alku’rani Kuma suna daga cikin malaman makarantar a yanzu.

Da ya ke jawabi Justice Jamilu Shehu Sulaiman Joji a babbar kotun jihar kano ya bayyana kadan daga irin darajar da dalibi ya ke samu idan ya sauke Alku’rani.

Malami mai jawabi a yayin taron Sheikh Urwatu Ja’afar ya yi jawabi mai tsawo Kan falalar karatun Alku’rani mai girma a addinin musulunci.

A yayin taron an kaddamar littafi mai suna Shawarwari 30 ga iyaye wajen samun ilmi mai albarka Wanda shugaban makarantar alaramma Muhammad Sadisu ya wallafa.

Shi kuwa Mai unguwar Shekar maidaki Alhaji Badamasi ya bayyana farin cikinsa bisa samun irin wadannan makarantu a yankin.

Leave a Comment