Labaran Jiha Manyan Labarai

Kisan Ummulkhulsum Sani: Za’a Gurfanar da Geng Quarong a Kotu a 4 ga Oktoban 2022

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Mustapha Gambo Muhammad

Babbar Kotun Jihar Kano, karkashin jagorancin Alkali Sanusi Ado Ma’aji ta tsayar da ranar Hudu ga watan Oktoba, 2022 a matsayin ranar da za’a fara gurfanar da Dan kasar Sin, Geng Quarong wanda ake tuhuma da kashe wata Mata Ummulkhulsum Sani Buhari a dakinta.

A yayin zaman na ranar Alhamis din nan Wakilinmu na kotu da yan sanda ya ruwaito mana cewar, wanda ake tuhuma ya roki kotu da ta dage zamanta domin ya samu lauyan da zai tsaya masa.

A nasa bangaren, Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barrister Musa Abdullahi Lawan bai soki rokon da Quarong ya yi ba.

Ku karanta: Abduljabbar: Kotu ta Sanya Ranar Karbar Rubutattun Hujjojin karshen na Kowanne Bangare

Ya ce ya zama dole kotu ta dage zamanta domin Wanda ake tuhuma ya samo lauyan da zai tsaya masa, duba da girman laifin da ya aikata.

Ya bukaci kotun da ta dage zamanta.

Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji Ya dage Shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba domin a gurfanar da Quarong, ya Kuma umarci da a ajiye wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali da tarbiya.

Leave a Comment