Siyasa

Kiru-Bebeji: Zamu Tabbatar NNPP Ta Yi Nasara A Dukkan Matakai — Abdulmumin Kofa

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Zakariyya Adam Jigirya

Dan takarar Majalisar wakilai ta Tarayya Mai wakiltar Kananan hukumomin Kiru da Bebeji Alhaji Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce za su tabbatar jam’iyar NNPP ta yi nasara a dukkan Matakai a zabukan shekarar 2023 da ke tafe.

Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana hakan ne yayi kaddamar da yakin Neman zaben sa, taron wanda ya samu halartar dubban jama’ar yakin Kiru da Bebeji kuma aka gudanar a gidan sa dake garin kofa karamar hukumar Bebeji.

Yayin taron dai kofa yayi amfani da damar wajen karbar mutane sama da dubu biyu (2,000) wadanda suka koma jam’iyyar NNPP kwansiyyya kuma sakayi alakwarin aiki tukuru wajen bawa Dan takarar shugabancin kasar karkashin tutur NNPP Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso kuri’u miliyan biyar da kuma ganin jam’iyyar tayi nasara tun daga sama har kasa.

Ku karanta: Ina Neman Afuwar Duk Wanda Na Batawa — Hafizu Kawu

Taron ya samu halartar yan takarar majalissar jiha na Kiru Honarabil Abubakar Usman Rabula Dana Bebeji Honarabil Ali Muhammed Tiga da Hajiya Azumi Namadi Bebeji da Honarabil Gambo Sallau da Dankaka Usaini Bebeji da Shugabannin jam’iyyar NNPP na Kiru da Bebeji da Dattawan jam’iyyar da Matasa da Mata da sauran Al’ummar yankin wadanda suka fito kwansu da kwarkwata domin hallatar taron.

Leave a Comment