Da Dumi-Dumi

Kira Ga Gwamnati Kan Harkokin Sufuri Domin Tallafawa Direbobi

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar matuka motocin akorikura ta kasa reshen jihar Kano dake railway da a yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su taimakawa kungiyoyin sufuri duba da halin matsin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi a fadin kasar nan.

Shugaban Kungiyar ta kasa, Alh. Abubakar Dan’iya Bala ne yayi kira a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da cikar Najeriya 63 da samun ‘Yancin kai a ofishinsa dake Railway acikin birnin Kano.

Shugaban yac kara da cewa, Direbobi motocin haya suna cikin garari ta fannin ma’amullarsu da masu basu dakon kaya don kai musu wasu garuruwa, inda yace, Man Fetur yayi tashin gwauran Zabi wanda hakan ne ta sanya kwastomominsu ke ta korafi dangane da dan kudin da suka kara.

Ya kara da cewa, da yawa direbobin motocin haya sun hakura da daukar kayayyakin nesa saboda duk kudaden da suka samu suna tafiya ne a wajen siyan mai.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa, hakan ne ta sanya, kungiyar ta tara ‘ya’yanta ta yi musu bita akan su rika hakura da kadan domin saukakawa al’umma a bagarensu na harkokin sufuri.

Dan’iya ya bukaci hukumomi musamman masu ruwa da tsaki a bangare harkokin sufuri da su taimaka wajen waiwayar fannin, duba da yadda fannin yake ragewa gwamnati nauye nauye wajen samarwa matasa ayyukan yi da samar da kudaden haraji wanda hakan na daya daga cikin abubuwan dake kara habaka tattalin arziki.

Sannan yace, kasashen duniya da dama sun samu ci gaba ne ta bangaren sufuri da sauran bangarori inda yace yana mamaki da gwamnati ta yi watsi da harkokin sufuri a fadin kasar nan.

Shugaban ya kara da cewa, kungiyar tana shirya taron bita daga lokaci zuwa lokaci domin kara musu ilimi a bangarori harkokin Tuki da yadda za su tafiyar da motocinsu da mu’amulla da jami’an tsaro na kan hanya.

Abubakar Dan’iya Bala, ya bayyana cewa, kungiyar matuka motocin haya ta kasa, ta samu nasarori da dama da suka hadar da taimakawa ‘ya’yan kungiyar ta hanyar rage musu radadin rayuwar da aka tsinci kai a ciki, musamman iyalan wadanda suka rasu da marasa karfi da wadanda basu da mota da su tuka.

A don haka shugaban yake kira ga gwamnatoci a matakai daban daban, da su rika suyo motocin haya suna baiwa kungiyoyin sufuri don baiwa ‘ya’yan kungiyoyinsu a matsayin tallafi tare da hadawa Gwamnatin kudaden motocin, wanda idon aka yi haka an taimakawa rayuwarsu.

Daga karshe ya jaddada kudirinta kungiyar na ci gaba da baiwa gwamnatin cikakken hadin kan da suka kamata wajen bunkasa harkokin sufuri a jihar Kano da kuma Kasar baki daya.

Ya kuma bukaci kungiyoyin sufuri da su kara hada kai wajen wayar da kan’ya’yan kungiyoyin su na sufuri ta yadda za su yi gogayya da sauran takwarorinsu na kasashen ketare.

Leave a Comment