Da Dumi-Dumi

KAYAN ABINCI: Mun Samar Da Kayan Abinci A Farashi Mai Rangwami

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Shugaban kungiyar masu manya da kananan sana’o’i hannu na kasa reshan jahar Kano Alhaji Aminu Ibrahim ya bukaci al’umma da su garzaya harabar filin baje koli domin siyan kayan abinci cikin farashi Mai sauki.

Ibrahim ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai dake fadar gwamnatin jihar Kano a ofishin kungiyar dake kan titin Gidan Zoo.

Ibrahim ya ce kungiyar ce ta yi tsayin daka wajen tattaunawa da manya da kananan shuwagabannin kasuwannin Kano domin Samar da kayan abinci ga alummar jihar Kano akan rangwamin farashi ta hanyar kawo kayan abincin a filin baje kuli domin siyarwa.

Ya kuma ce dukkannin kasuwannin jahar Kano sun amince da samar da kayan abinci a filin na baje koli akan farashi mai rangwami ga al’umma.

ya kara da kira ga al’umma da su garzaya filin baje koli domin siyan kayan abincin cikin rahusa.

Malam sulaiman sabo fagge na daga cikin Wanda ya je filin na baje koli domin sayan shinkafa hakika ya samu farashi Mai rangwami wajen siyan kwano biyar na shinkafar.

Leave a Comment