Kasuwanci

KARANCIN FETIR: Muna Rokon Gwamnatin Tarayya ta Zauna Dillalan Man Fetir — Mamuda Zangon-kabo

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar yan kasuwa ta karamar hukumar kabo ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta zauna da Dillalan man fetur da sauran masu ruwa da tsaki a fannin man domin kawo daidaiton da zai kawo karshen wahalar man da ake fama da shi a jihohin kasar nan.

Daya daga cikin jagororin kungiyar Alhaji Mamuda zangon-kabo ne ya yi kiran lokacin da yake ganawa da manema labarai a nan Kano.

Zangon-kabo kabo ya ce zama da yan kasuwar da suke shigo da man yana da mutukar mahimmanci domin jin makasudu da yasa man yake wahalar samu da kuma tsada a wasu daga cikin gidajen man fetur.

Ya ce kamata yayi Gwamnati ta dauki mataki kasancewar matsalar ta shafi fannoni da dama ciki har da kasuwanci saboda farashin kayayyakin masarufi ya tashi a kasuwanni da kudaden ababen hawa, wanda ya jayo talakawa suke fuskantar kalubale da yawa.

Ku Karanta: Muna Rokon Gwamnatin Tarayya ta Tursasa Dillan Mai Sayarwa a Farashin Gwamnati — Masu Kayan Gwari

Ya ce zaman shine abin da zai kawo kyakyawar fahinta a tsakanin dukkan bangarorin da abin ya shafa da nufin samarwa alumma sauki a harkokin rayuwarsu ta yau da kullum.

Haka zalika, ya shawarci alumma kasar nan da su kasance masu gudanar da addu’oin samun sauki akan al’amura da suke damun su musamman matsalolin rashin tsaro daya zama ruwan dare gama duniya.

Ku Karanta: Bamu Ji Dadin Tsarin Takaita Cire Kudin Da CBN Ya Kawo Ba — Kungiyar Masu Safarar Dabbobin

Mamuda Zangon-kabo ce gwamnati tana da rawar takawa a fannoni da yawa kasancewar itace uwar kowa wadda take da hanyoyin da za ta samarwa alumma abubuwan more rayuwa da sauran kayayyaki da zai iya amfana.

Ya ce akwai bukatar alumma su rika yiwa su shugabannin su addu’oi domin basu kwarin gwiwar aiwatar ayyukan ci gaba mai dorewa.

Leave a Comment