Da Dumi-Dumi Labaran Jiha

Kano Ta Sake Tura Dalibai 150 Karo Karatu

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin jihar Kano ta sake tura dalibai 150 a Karo na uku zuwa kasar India domin Karo karatu na digiri na biyu

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da rukuni na uku na daliban da zasu tafi ƙasar India domin yin karatun digiri na biyu su ɗari da hamsin inda yanzu haka jimillar wadan da suka tafi sun kai adadin mutane 340 cikin mutun 1001 da aka tantance.

Gwamishinan harkokin ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata ne ya jagoranci rakiyar a safiyar yau cikin tsarin da gwamnatin Kano tayi na tura mutane ƙasashen waje domin ƙaro karatu.

Dakta Kofar Mata ya kuma buƙaci dukkan daliban da su kasance jakadu na gari.

Da yake jawabi yayin bankwana da ɗaliban Kwamishinan yaɗa labarai na kano Baba Halilu Ɗantiye ya ce ɗaliban da aka tura domin ƙaro karatu an turasu ne domin ana ganin sun cancanta

Wakilinmu na fadar gwamnatin jahar Kano Adamu Dabo ya rawaito cewa gwamnatin Kano tace zata tabbatar da dukkan ɗaliban da aka tantance su tafi domin ƙaro karatun digiri na biyu.

Leave a Comment