Labaran Jiha Manyan Labarai

Kano Ta Kaddamar Da Shirye-shiryen Aikin Hajjin Shekarar 2024

Written by Pyramid FM Kano

Daga: YAKUBU ABUBAKAR GWAGWARWA

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kaddamar da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2024 a hukumance a ranar Alhamis din nan.

Darakta Janar na hukumar Alhaji Laminu Rabi’u ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai, wanda ke alamta fara shirye-shiryen aikin na bana a gudanar a ofishinsa .

Ya ce hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware kujeru 5,934 ga jihar Kano.

A cewarsa, bisa umarnin hukumar NAHCON, kashi 60 cikin 100 na kujerun aikin Hajjin bana za a baiwa alhazai ne yayin da za a baiwa maniyatan dake adashin gata a karkashin bankin musulunci na Ja’iz kashi 40 cikin 100.

Har ila yau, Darakta Janar din ya sanar da Naira miliyan 4 da rabi a matsayin kudin da maniyata zasu fara jiyawa na aikin Hajjin badi, inda ya kara da cewa wadanda ba za su iya ba to su hanzarta shiga shirin adashin gata.

Ya ce “mun kaddamar da shirin tsare-tsaren aikin Hajjin 2024 a yau. Mun kaddamar da siyar da kujerun ne bayan mun kammala rabon kashi 60 na kujerun zuwa kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

“Mun umurci jami’an alhazai na kananan hukumomi da su fara karbar kudaden ajiya daga maniyyatan da ke da niyar zuwa kasar mai tsari domin sauke farali,” inji shi.

Rabi’u Danbappa ya kuma ce hukumar ta tashi tsaye wajen ganin an mangace dukkan kalubalen da aka fuskanta a aikin Hajjin 2023 domin gudanar da aikin na bana cikin nasara.

Leave a Comment