Labaran Jiha Muhalli

Kano Ta Bukaci Ma’aikatun Sakatariyar Audu Bako Su Kula Da Muhalli

Written by Admin

Daga: SANI MAGAJI GARKO 

Gwamnatin Jihar Kano ta ce, tsaftar muhallin sakatariyar Audu Bako ta kasance ba yabo ba fallasa la’akari da yadda Ma’aikatu da dama suke cike da tsafta, amma bandakunan su babu ruwa.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Alhaji Nasiru Sule Garo wanda ya jagoranci zagayen duba ma’aikatu da hukumomin gwamnati a sakatariyar ta Audu Bako, ya bukaci Kwamishinonin da ma’aikatun su ke a sakatariyar, da su hada kai don tsaftace ta.

A yayin tsaftar muhallin ta juma’ar karshen wata, an ziyarci hukumar kula da harkokin Ma’aikata ta jihar (Kano State Civil Service Commission) da Ofishin shugaban ma’aikatar jihar Kano da Ma’aikatar yada labarai da kuma ofishin babban mai binciken kudi na jihar wacce dukkaninsu aka samu ko dai babu ruwa a bandakunan su, ko kuma aka sami Datti a ma’aikatun.

“Kamar kullum, yau ma matsalar iri daya ce, wato ta bandakuna. Kamar gurare biyu da muka je wata ofishin mai binciken kudi da na ma’aikatar yada labarai bandakunan su ba yabo ba fallasa. Amma na ofishin shugaban ma’aikata da na hukumar kula da harkokin Ma’aikata, duk bandakunan su babu tsaftar sannan babu ruwa, hakan bamu ji dadinsa ba,” inji Garo.

“Na dade ina fada, bandaki guri ne da baka san lokacin da zata bukace shi ba kuma tabbatar da tsaftarsa yana da matukar muhimmanci,” ya ce.

Kwamishinan ya kuma bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin tsaftar muhallin na yau Asabar don sharewa tare da tsaftace yankunan su, ya na mai cewa, matukar mutane suka zauna a gida kuma basu tsaftace shi ba hakan ka iya bawa kananan cututtuka damar yaduwa.

“Muna yabawa al’ummar jihar Kano bisa irin hadin kan da suke bamu na zama a gida a lokacin tsaftar muhallin wacce take farawa daga karfe 7 zuwa 10 na safe, to amma ba wai zaman gidan bane kawai kowa yayi amfani da lokacin wajen yashe magudanan ruwa da tsaftace muhalli domin sai kowa yaba da gudun mowa sannan za’a samu nasarar da ake da bukata” inji Kwamishinan.

Leave a Comment