Labaran Jiha

KANO: Chidari Ya Mika Ta’aziyar Rasuwar Mahaifin Shugaban Ma’aikata.

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muhammad Adamu Abubakar

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano  Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai, da Yan uwan shugaban ma’aikata na jihar Kano Alhaji Usman Bala bisa Rasuwar Mahaifin sa Alhaji Bala Muhd ​​Tajuddeen.

Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran zauren majalissar dokoki ta jihar Kano Uba Abdullahi ya fitar ya Kuma rabawa manema labarai.

Ku karanta: Ganduje Ya tura Sunan Ali Burum-Burum Majalisa don Nada shi Kwamishina

Sanarwar ta ambato shugaban majalisar Chidari ya na cewa marigayin ya gudanar da rayuwar da ta dace a yi koyi da shi, domin ya sadaukar da rayuwarsa ga bautar Allah da gaske kuma a koda yaushe yana kan gaba wajen bayar da taimako ga mabukata a kowanne lokaci.

Chidari ya ci gaba da cewa majalisar ta samu labarin rasuwarsa cikin kaduwa tare da addu’ar Allah SWT ya sa Aljanna ce makomar sa.

Daga nan Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari a madadin ‘yan majalisar ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje da daukacin Ma’aikatun Gwamnati da Iyalan Marigayi bisa babban rashin da suka yi.

Leave a Comment