Yanzu-Yanzu

Kamfanin Galaxy Backbone na bajekolin ayyukansa A babban taron cibiyar sadarwa ta Kasa

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Mustapha Gambo Muhammad

Shugaban Hukumar Adana Bayanan Sadarwa na Kasa, (Galaxy Backbone) farfesa Muhammad Bello Abubakar ya bayyana cewar a yanzu haka Hukumar na halartar babban taron cibiyar harkokin sadarwa da fasahar zamani da tattalin arziki Karo na gama wanda a yanzu haka ake gudanarwa a Badun, Babban Birnin Jihar Oyo.

A cikin wani jawabi da Shugaban Hukumar, Farfesa Muhammad Bello Abubakar ya sanyawa hannu ya bayyana cewar taken taron na bana shi ne ‘ Yadda za’a Iya yin amfani da fasahar sadarwa wajen bunkasa tattalin arziki harma da na kananan masana,antu.

Yace Cibiyar Adana Bayanan fasahar Sadarwa ta Kasa ta samar da ingantatun kayayyakin aiki irin na zamani sannan a cewarsa Hukumar tana samar da bayanai ga hukumomin da ma’aikatun gwamnatin tarayya da ma kamfanoni Yan kasuwa masu zaman kansu domin inganta ayyukansu ta hanyoyiyin da suke bukata dai dai da zamani.

Yace daga cikin ayyukan da hukumar ke yi sun hadar da samar da adana bayanan da samar da tsaro akan harkokin da suka shafi fasahar sadarwa da inganta harkokin sadarwa a maaikatu da hukumomin gwamnati da gidaje dake birnin tarayya Abuja.

Shugaban ya kuma ce hukumar na samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ga Yan kasuwa.

Ya kara da cewar daga cikin ayyukan hukumar sun hadar da samar da ingantattun yanayi kula da tare da kare dukkanin abubuwan da ya kamata hukumomi da maaikatu da masu zaman kansu.

Ku Karanta: Muna Bukatar Tallafin Gwamnatin Kano Inji Kungiyar Masu Kayar Gwari

Farfesa Muhammad ya ce hukumar Adana Bayanan ta Kasa ta samar da yanayin saka hannun jari don bunkasa tattalin arzikin Kasa.

Farfesa Muhammad Bello Abubakar ta na amfanin da babban taron domin bajekolin fasaha da kuma kirkira da take, wanda hakan kuma zai taimaka Najeriya ta cimma kudirinta na shirin bunkasa tattalin arziki 2020-2030.

Leave a Comment