Yanzu-Yanzu

Kafa gidan zakka hanya ce ta tallafawa raunana a musulunc – Prof. Maibishra.

Shugaban hukumar Zakka da Hubsi ta jihar kano Farfesa Ibrahim mu’azzam Maibishra ya yaba wa gwamnatin jihar kano bisa Samar da wuri na din din din ga hukumar.

Farfesa Ibrahim mu’azzam Maibishra ya bayyana haka ne yayin kaddamar da rabon Zakka ga mabukata a bana kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a nan Kano.

Ya ce Samar da matsuguni na din din din ga hukumar zai tallafawa hukumar a sha’anin tattara kudaden Zakka daga mawadata a jihar.

Farfesa Maibishra ya bukaci mawadata da su cika umarnin Allah wajen mika ta su zakkar ga hukumar domin raba ta ga mabukata kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

A Jawabin sa babban Darakta a hukumar ta Zakka da Hubsi ta jiha Alhaji Garba Musa ya yaba wa gwamnatin jihar kano bisa Samar da matsuguni na din din din ga hukumar a wannan lokaci tun bayan kafa hukumar shekaru 20 da suka gabata.

A yayin taron Sheikh Abdulwahab Abdallah Gadon kaya da Sheikh Nura Arzai sun gabatar da jawabi Mai tsawo Kan muhimmacin ba da Zakka a addinin musulunci kasancewar ta ta biyu cikin rukunan addinin musulunci guda biyar.

Sun Kuma ja hankalin wadanda suka amfana da tallafin zakkar da su cigaba da yi wa wadanda suka ba da zakkar.

Taron raba zakkar a wannan lokaci ya biyo bayan ba da tallafin naira miliyan 10 ga hukumar daga Alhaji Aminu Alhassan Dantata domin raba wa ga mabukata. Yayin da Kuma gwamnatin jihar kano ta yi alkawarin bayar da naira miliyan 35.

Leave a Comment