Kasuwanci

JIHAR KANO: Zamu Farfado Da Kasuwanci Ta Hanyar Zamani

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin jihar Kano tasha alwashin farfado da harkokin inganta kasuwancin zamani domin cigaban al’umma.

Alwashin ya fito ne daga bakin mai baiwa Gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin kasuwanci Hon. Nura Hussaini wanda aka fi sani da (President) a yayin zantawa da manema labarai.

Hussaini yace, ganin yadda a yanzu mafi akasarin ababan da ake harkokin kasuwanci dasu daga kasashen ketare a ke shigo dasu. Haka zalika babu abinda jihar Kano ke fitarwa na azo agani a fadin duniya.

President, ya kara tabbatar ma al’umma cewa, farfado da masana’antun da gwamnan zai yi zai taimaka matuka wajen samarwa jama’ar Kano cigaba da ayyukan yi da bunkasa harkokin Kasuwanci a Kasa baki daya.

Ya Kuma kara da cewa, gwamna Abba Kabir Yusuf mutum ne mai san gaskiya da rikon amana a rayuwar sa, dan haka dole ne, suma su rike masa amana tare da aiki tukuru.

Hon Nura, ya kuma kara da batun kwanakin da gwamna yayi na farko da akafi sani da kwana 100 farko a ofis ya gabatar da ayyuka daban-daban a ciki da wajen jihar Kano da ya tabbatar ya zo ma da Kanawa abin alkhairi.

Daga karshe, ya taya Gwamna Abba murnar samun nasara a kotun koli da kuma bukatar a yanzu al’umma su dage da addu’a ga Gwamna wajen cigaba da gudanar da ayyukan alkhairi ga jama’ar wannan Jiha.

Leave a Comment