Da Dumi-Dumi Kasuwanci Labaran Jiha

JIHAR KANO: Harkokin Tsaro Ga Kasuwanninmu Na Daga Cikin Kalubalenmu

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Anyi kira ga manya da kananan ‘yan kasuwa da su hada hannu domin inganta harkokin cigaban kasuwanci a fadin jihar Kano.

Kiran ya fito ne daga shugaban Kasuwar ‘Yankaba dake karamar hukumar Nassarawa Alhaji Aminu Lawan Nagawo yayin zantawarsa da manema labarai .

Nagawo yace, akwai tsari na habbaka kasuwanci musamman don cigaban tattalin arzikin jahar Kano.

Ya kuma, mika godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa nasarar da yasamu ta tabbatar da shi a matsayin gwamnan jihar Kano da Kotun Koki tayi, tare da kira ga al’ummar jihar Kano da su taimakawa gwamnati wajen inganta harkokin tsaro, ilimi da kuma kasuwanci a fadin jihar Kano.

Leave a Comment