Yanzu-Yanzu

Jihar jigawa Zata Cigaba da Samar da Ayyukan raya Kasa – ALGON

 

By: Kabir Getso

Shugaban karamar hukumar Dutse kuma shugaban shuwagabannin kananan hukumomi na jihar Jigawa, Hon Bala Usman Chamo ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa dake helikwatar karamar hukumar ta Dutse.

Hon. Usman yace gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar yayi namijin kokari wajen hidimtawa al’ummar jahar da aikace aikacen Raya kasa iri daban daban,wada hakan yasa al’umma sukai fitar Dango wajen zabar Jam’iyyar APC a dukkanin Zabukan da suka gabata.

shugaban karamar hukumar ya Kara da yin kira ga jamaa dasu maida hankali wajen yashe magudanan ruwa Dan kada asake maimaita ambaliyar ruwa a damunar da ta gaba ta.

Hon Bala Chamo ya yi kira ga al’ummar jihar ta Jigawa dasu bawa gwamnati Mai zuwa cikakken hadin Kai da goyon bayan don cigaba da bujuro da sabbin Ayyukan raya kasa.

Leave a Comment