Labaran Jiha Nishadi Yanzu-Yanzu

Jarumin Kannywood Umar Yahay Bankaura Ya Rasu Bayan Doguwar Jiyya

Written by Pyramid FM Kano

Sanan nan Jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Umar Yahaya Malumfashi ko Kuma Bankaura kamar yadda aka fi sanin sa ya Rasu bayan fama da Doguwar Jiyya.

Marigayin Wanda a baya-bayan nan yayi shura da sunan Yakubu Kafi-gwamna a cikin shirin nan Mai dogon zango na Kwana Casa’in na gidan Talabijin din Arewa24 ya rasu bayan fama da rashin lafiya, lamarin a kwanakin bayan hotunan sa suka karade shafukan sada zumunta inda a cikin ake Neman al’umma su taya shi da Addu’a samakaon rashi lafiya da yake fama da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin yayi doguwar jinya a Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala dake cikin kwaryar birnin Kano.

Ku karanta: KANO: Chidari Ya Mika Ta’aziyar Rasuwar Mahaifin Shugaban Ma’aikata.

Kuma a nan ne ake zaton ya rasu.

Tuni dai jarumai da masu shirya fina-finan Hausa a Kannywood kamar su Falalu A Dorayi da Ambasada Auwalu Muhammad Danlarabawa suka wallafa hoton marigayin a shafukansu na sada zumunta na zamani inda suke masa adduar Allah ya jikansa.

Leave a Comment