Da Dumi-Dumi

Jan Hankali Ga Mahukunta Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kano Pillars Da Masu Ruwa Da Tsaki

Written by Pyramid FM Kano

Daga: MUSTAPHA GAMBO MUHAMMAD

Yana da kyau a kafa kwamitin bincike domin gano wannan katuwar matsalar da take tattare da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da rashin cigaban yaran mu da za su iya bawa kungiyar gudunmawa domin gano yadda za’ayi maganin ta tun bata je gabar da ba za’ayi maganinta ba.

Da farko duk wanda yake da kukami a ko wane rabe Rabe Da Kungiyar Take Da Shi Ma’ana Kano Pillars, Junior Pillars, U15 da U13 da kuma kwamitoci da aka yi babu wanda ba a bawa takarda ba kuma babu wanda bai san hurumin sa na aiki ba. Ni a nawa binciken da na ii wanda nake jawo hankali a kan a yi ta hanyar tantance duka ‘yan wasan kungiyar ma’ana a duba takardun kwantiragin su domin gane wanda suke mallakin kungiyar da Kuma Mallakin ejoji ma’ana agents saboda tun daga lokacin mai horarwa na baya da ya tafi wato Coach Evans Ogenyi zuwa yanzu akwai wani mutum guda da ba shi da mukamin komai a kungiyar amma kuma ya nada kan sa da kan sa al matsayin Firotokol na duk mai horawar da zai zo kungiyar ma’ana mai masaukin mai horarwa domin ko a baya shi yake yawo da wancan Coach Evans Ogenyi din yake masa hidima yanzu m ya dora kamar yadda yake a baya duk da an samu canjin mai horarwa wanda hakan ta kai daga wancan lokacin zuwa yanzu yana da ‘yan wasa mallakin sa mi iyaka wanda bincike na ya nuna mutum 8 wanda na san idan aka yi wancan binciken da na bada shawara a yi al sama za’a iya samun sama da haka wanda wasu ma a baya mallakin Klkungiyar Nlne amma ya dawo ya mallake su suka dawo karkashin sa wanda ta kai ko wasa za’a yi daga farkon wasan zuwa karshe yana nan kasawa yake ya tsare sai an saka masa a kalla mutum 5 wanda wannan abu ya jawo tauye hakkin wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar da dama wanda kuma barin haka zai zama a shekara biyu zai iya mallake kungiyar kamar yadda Coach Bros ya mallake kungiyar kwallon kafa ta Plateau United da ke garin Jos wanda hakan ya jawo a garin Jos ya cutar da duk wani ko wasu da suke harkar kwallo. Wnnan shine yasa ni a karan kaina a nan Kano ce ba za mu bari muna gani al’ummar mu su cutu ba. Kuma wannan mutumi da nake magana a kai yana da wata kungiya irin ta hade-hade da sunan ta yake da wadannan harufan a ciki “MELRE” domin a kasa da wata uku naya mun yi  wasa da su a filin mu sai naga ai wajan mutum 4 wanda da ba a Kano Pillars suke ba yanzu duk a daukar nan da aka yi suna cikin kungiyar an dauke su wannan shine ya kara tabbatar mun da bincike kuma wannan shine dalilin da yasa za ka ga duk kyan yara ba sa samun kungiyoyi saboda irin bata harkar kwallo din da irin wadannan mutumin suka yi kuma ka ga wanda ma ba su kai ba kuma ana daukar su harma ta kai ana iya saka su.

A karshe ina rokon wanda abun ya shafa da su yi bincike as kai domin daukar mataki idan kuma sun kasa to tunda kungiyar a karkashin Jahar Kano take to zamu aike da wannan korafi zuwa hukumar karbar korafi ta Jahar Kano domin ita ta zo ta yi da kan ta tunda dama tana da kwararrun mutane da suka je har Kasar waje suka dauko horo na bincike.

Nagode Nagode Nagode
Mukhtar Abdullahi Shu’aibu
abdullahimukhtar79@gmail.com
14-09-2023

[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

Leave a Comment