Manyan Labarai Yanzu-Yanzu

Jam’iyyar PDP Ta Hade Kan Al’ummar karamar Hukumar Shira – Maliya

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Shugaban riko Na karamar Hukumar Shira dake Jihar Bauchi Alh. Babangida Maliya ya bayyanna cewa yanzu karamar Hukumar Shira ta jam’iyyar PDP ce, sabanin a baya yadda ake ganin jam’iyyar adawa na da tasiri a yankin.

Maliya ya bayyanna hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a sakariyar karamar Hukumar ta Shira yace tun bayan zuwan shi hugabancin riko na karamar hukumar yake kokarin kyautatawa mutanen yankin ta fuskar bijiro da sabbin Aayyukan raya kasa, inganta asibitoci, farafado da harkar ilimi, inganta tsaro da kuma farfado kasuwanci.

Babangida Maliya yace a baya an wayi gari Sakariyar karamar Hukumar ta Shira ta zama kamar Kkufai babu kowa saboda rashin tsaro da fargabar abinda kan iya zuwa ya dawo,amma zuwansa karamar Hukumar wannan abu ya zama tarihi, mun gyara dukkanin gine-ginen da ke karamar Hukumar tare da zuba kayayyakin ofisoshi da sauran kayayyakin alatu inji shi.

Maliya, ya yabawa Gwamnan Jihar Bauchi Sen. Bala Mohd Kauran Bauchi bisa irin aikace aikacen da yake wa jihar wanda hakan yasa al’ummar Jihar Bauchi suka kara bashi dama domin dorawa zuwa wa’adin mulki na biyu, gwamnan na iya kokarinsa wajen bawa shuwagabannin riko kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi domin suyi aikace aikacen da zasu sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ga al’ummar yankin.

Maliya yayi kira ga daukacin al’ummar Jihar Bauchi da su cigaba da bawa gwamnan cikakken hadin kai da goyon baya domin cigaba da ayyukan da zai taimaki al’ummar Jihar Bauchi baki daya, tare da tabbatar wasu yankin da ayyukan baizo gare su ba, da su cigaba da hakuri nan bada dadewa ba aikin zai zo gare su.

Leave a Comment