Siyasa

Jam’iyun PRP, ZLP, NRM, APM da AAC a yankin Arewacin Kano sun amince domin marawa Sanata Barau na APC baya

By: Mukhtar Yahaya Shehu

Gamayyar ‘yan takarar kujerar Dan majalisar Dattijai daga yankin Kano ta Kudu na jam’iyun PRP da ZLP da NRM da APM da Kuma AAC sun amince domin marawa Sanata Barau Jibri na jami’yyar APC baya a zaben ranar Asabar Mai zuwa.

A yayin taron manema labarai Dangane da haka,Dr Aliyu Zakirai daga jami’yyar PRP ya bayyana cewa sun amince domin marawa Sanata Barau Jibri baya a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a Asabar 25 ga wannan wata na fabrairu.

” Matukar za a yi la’akari da kwarewar Sanata Barau Jibri a fannin ayyukan raya kasa a yankin Kano ta Arewa ya Sanya muka amince domin mara masa baya”. In ji Dr. Aliyu Zakirai.

Gamayyar ‘yan takarar kujerar Sanata a Arewacin Kano sun Kuma yabawa sanata Barau Jibri bisa Samar da irin wadacan ayyukan raya kasa a yankin da suka hadar da gyaran titin Kabuga zuwa Dayi da Samar da kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya a garin Kabo da aikin daga darajar kwalejin koyar da aikin gona ta Dambatta zuwa jami’a da takwarar ta horas da malamai da ke Bichi da Kuma Samar da cibiyoyin jami’ar koyar da Ilmi daga gida a kananan hukumomi 13 dake yankin.
End.

Leave a Comment