Ilimi

Jami’ar Tarayya Ta Dutsin-ma FUDMA Tace Ingantaccen Karatun Digiri AKCOE Ta Ke Bayarwa

Written by Pyramid FM Kano

Daga: JAMILA SULEIMAN ALIYU

Jami’ar tarayya ta Dutsin-ma (FUDMA) ta nuna gamsuwarta da tsarin da makarantar kwalejin ilmi ta Aminu Kano AkCOE tayi don tunkarar fara bayar da karatun digiri a kwasa-kwasai goma sha daya da suka samu sahalewar su fara gudanarwa jingine ta Jami’ar.

Shugaban Jami’ar tarayyar Farfesa Arma Ya’u Bichi ne ya bayyana hakan yayin da suka kawo ziyarar gani da ido domin duba tsare tsaren makarantar ko yayi daidai da ka’i’dojin da jami’ar ta gindaya tare da nuna yabo mai yawa da kuma cancantar kwalejin da ta ci gaba da gudanar da harkokin karatunsu ka’in-da-na’in tare da yabo mai yawa akan ragin da makarantar tayi na kaso hamsin cikin dari wanda yace hakan zai taimakawa marasa karfi su amfana da karatun na digiri.

Farfesa Arma Ya’u ya kuma mika rokon jami’ar ga gwamnatin Kano da ta tallafawa makarantar ta fuskar matsuguni na din din din domin gwamnatin jihar Kano tayi fice wajen tallafawa ilmi in da yace fatan gwamnatin Kano zata waiwayi makarantar domin tana tallafawa ‘yan asalin jihar. Farfesa Bichi ya ce, fannin dalibai sun tantance sun ga komai yayi dai dai da tsarin (FUDMA). Shima a nasa bangaren shugaban makarantar Dr. Ayuba ya nuna farin cikinsa da irin yabon da kwalejin ta samu duk da suna tsaka da ayyukan samar da ofisoshi da sauran gine-gine domin tafiyar da harkokin koyo da koyarwa na kwalejin da sukayi hadin gwuiwa da jami’ar tarayya ta Dutsin-ma dake Katsina tare da yin fatan alheri ga jami’ai da ga jami’ar tarayya ta Dutsin-ma da suka kawo ziyarar gani da ido da kuma fatan nasara.

Leave a Comment